Yanda zaka karanta sakon da aka goge koda ana amfani da GB whatsapp

 


Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi. Yan'uwa cikin ikon Allah yau na kawo mana wani application da zai magance mana matsaloli kala daban daban wadanda muke da buqatar su tun asali.

Da yawa akwai wadanda suke buqatar ganin dukkanin sakon ko messages da aka turo aka goge a whatsapp ko sauran social media kamar Telegram da massenger na facebook. Sannan koda mutum tana amfani da whatsapp GB. To da zarar ka mallaki wannan spplication din zai baka damar mallakar dukkanin sakon da aka turo sannan aka goge na rubutu ne ko hoto ko decument ko wani file haka.

Bugu da kari wannan application zai dawo ma da duk wani abu da aka taba turo ba daga baya ka goge su kamar video ko hoto a whatsapp koda ya sauka akan wayar ka zaka iya dawowa da su duk adadin kwanaki ko watannin da sukayi kai idan kayi sa'a ma koda shekara sukayi.

Saboda akwai irin wata takarda ko hoton da za'a iya tura ma ta whatsapp sannan kana ganin sa akan wayar ka normal sai daga baya ka nemi shi ka rasa. Saboda an riga da an goge ko kuma kai ka goge baka sani ba. To shi wannan application din zai baka damar dawo da duk wani abu da aka taba turama inde ta whatsapp ne da sauran social media.

Abin burgewar anan shine wannan application din gaba daya babu wani abin wahala a ciki wajen saita shi.

Kana dakko shi kawai zai bude ma sannan wajen amfani da shi babu wahala.

Amman ka sani ba wai zakaga abin da aka goge ma bane bayan farko baka saka application din a wayar ka ba.

A'a sai ka fara saka application din sannan zaiyi ma dukkanin wasu abubuwa da na lissafa a baya.

Kaje kasa zakaga na rubuta download sai ka taba shine zaka sauke application din a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post