Yanda zaka tura komai a wayar ka zuwa computer batare da Cable ba😍🥰.

 Assalamu alaikum yan'uwa barkan mu da juma'a. Ina fatan anyi sallah lafiya. Yan'uwa kada mu manta da yawaita salati ga fiyayyen halitta Da karanta suratul kahfi.

Yan'uwa wani application ne mai matuqar amfani da kuma abin mamakin da yaka mata ka mallake shi.

Zai baka damar tura duk abinda kake so daga computer zuwa waya ko daga waya zuwa computer batare da kayi amfani da cable ba.

Sanin kowane inde mutum zayyi turi a computer dole sai ya hada wayar da Cable sannan zai iya tura komai zuwa wayar ko computer.

To shi wannan application din zaka iya tura komai batare da kayi amfani da cable ba.

Ku biyo mu daya bayan daya acikin rubutun zan yi muku yanda ake amfani da wannan application din.


Da farko de na ajje muku link din wannan application achan kasa sai kuje ku dakko shi a wayar ku. Kana dakko shi kawai babu wani wahalar option ko hanyoyi a cikin sa. Kawai zai nuno ma Start ne idan ka danna kuma zai nuno ma Stop.

Bayan ka dakko application din abinda zakayi shine zakayi connect ko nace zaka hada wayar taka da computer din bangaren WIFI. Nasan kowa ya iya wannan.

Amman duba da yanda bakowane ya iya ba zan danyi bayani a takaice yanda ake hada wireless ko nace Hotspot na waya da computer.

Da farko a wayar taka zaka janyo sama zakaga an rubuta HOTSPOT kode wani abu makamanchin haka to sai ka danne gurin shine zai bude ma asalin inda yake acikin setting. Saboda idan nace zanyi muku bayan nemo shi acikin setting to bayanin zaiyi nisa sosai. Bayan ka danne shi ya bude ma to amfanin Dannewar shine may be Hotspot din akwai security to a wajen zakaga security amman idan ka tabbatar da Hotspot din wayar taka babu security kawai sai ka kunna shi tun farkon inda nace ku danna. Kamar de yanda kuka kunna Datar wayar ku. To bayan ka kunna hotspot din a computer sai ka kunna wifi dinta.

Idann ka kunna Wifi din shine zai bada damar hada wannan hotspot din wayar da wifi din computer. Shi kuma wifi na computer normal inda kake ganin chajin computer yake tafiya zakaga alamar Service to sai ka taba kana tabawa zata nunoma wannan Hotspot na wayar da ka kunna a farko. Sai kayi connect din kashi kuma kode ya tambaye ka Password daman tun farko nayi muku gayanin yanda zakuga passowors din Hotspot din wayar taka.

Bayan ka hada connect din wayar da computer na wifi.

Sai ka bude application din wayar taka.

Bayan k bude zai nuno ma kamar yanda zan ajje muku hoto a kasa.

👇👇👇👇👇👇👇


Bayan ya nuno ma haka sai ka Taba START din nan kamar yanda kuka ga hoton sama👆👆👆.

Bayan ka danna start din zai nuno ma haka. Ga hoto nan a kasa👇👇👇👇.



To bayan ya nuno ma haka zakuga ya rubuta STOP. Sannan da wasu bayanai kamar yanda kuke gani a hoton sama da na saka 👆👆👆👆.

Bayan nan a hoton sama idan kukayi la'akari zakuga na gewaye wasu numbobi da JAN abu to wadannan numbobin dasu zakayi amfani a computer ka. 

Amman bayan ya nuno ma haka inde tura abu zakayi to kada ka fita daga wayar taka koda minimize ne. Ko ka ce zaka kunna data ko wani abu. 

Saboda koda kayi connect din idan kayi kokarin yin hakan wayar zaka iya Katsewa.

To wancan abin da na gewaye ko nace numbobin nan zaku gansu kamar haka. (ftp://192.168.43.1:2221) ba lalle ya nuna ma daidai irin wannan da nayi muku misali ba. Amman de haka zai nuna ma. 

To sai kaje computer taka ka bude duk inda kake so ka bude kamar zaka bude Folder kenan.

Ga misalin sa nan acikin hoto a kasa.

👇👇👇👇👇

Kamar haka kenan. 

To abinda zakayi sai kayi kamar yanda zan nuna muku acikin hoton kasa.

👇👇👇👇👇

Acikin hoton da na dora muku a sama zaku ga cikin computer da muka bude ne sannan zakuga na gewaye shi da wata Alama Ja.
To daidai nan zaka zuba wannan Code din da application din ya baka.
Wanda na rubuta muku ko na baku misalan su a sama.
Idan kuka lita da kyu acikin hoton sama zakuga na zuba wannan code din na application din.
To daida zaka bi a hankali ka rubuta. Bayan k rubuta kawai sai ka Danna Enter a jikin Keyboard din computer ka.
Kana danna Enter zakaga  wayar taka ta bude acikin computer.
To normal sai ka qara bude wani Windows din acikin computer din taka saboda kada ka kulle wannan connect din da kayi.
Kawai duk abinda ka Janyo ka dora a daidai wannan connect din normal zaka tura shi a wayar ko a computer Sharp.

Kada kaga rubutun yayi yawa wallahi Acikin mintuna zakayi wannan abin da na fada muku.

Ga link din application din a kasa sai kaje ka dakko shi kayi amfani da shi


👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post