YANDA ZAKAYI CHAT DA KOWANE YARE NA DUNIYA



 YANDA ZAKAYI CHAT DA KOWANE YARE NA DUNIYA


Cikin wannan darasin yau zanyi mana cikakken bayanin yadda zaka iya yin chat da kowane irin yare na na duniya baki daya da Yaren da kasani harma da Yaren da baka sani ba.

Abun da ake buƙata da mai sauraro ko mai karantawa ka tsaya ka karanta wannan bayani daga farkonsa zuwa ƙarshe sai dai wata ƙila wasu zasu iya tunanin sun san wannan Application ɗin,to gaskiya wannan Application ɗin application ne sabo ba kamar wanda muka taɓa yin bayaninsa ba a baya,kuma zanyi mana bayani akan Application ne guda biyu saboda muje bayani na Application ɗin farko batare da na tsawaita bayani ba.

Application na farko

Wannan Application yana baka damar yin chat da duk Yaren duniya kuma ba wai yare kaÉ—ai ba zai fassara maka duk wani rubutu da baka iya fahimta ya mayar dashi zuwa Yaren da kake iya ganewa.

Yanda ake anfani da wannan Application É—in 


Bayan ka dauko shi daga link ɗin da zan ajiye muku aƙasa kawai sai kayi copy na text ɗin da kake so ya fassara maka sai ka seta shi zuwa yaren da kake so sai ka koma whatsApp ko chat ɗin kake yi sai paste shi kenan idan akayi maka reply sai ƙara copy na text ɗin sai ka koma cikin wannan Application kayi paste shi app ɗin zai fassara maka sai ka sake copy ɗinsa haka zakayi.

Application na biyu 

Application na biyu shi kuma sunansa Gboard wanda yafi na farko sauƙin aiki kawai abinda zakayi shine zaka san wane yare ne yake maka magana na dashi kaikuma dama kayi installing ɗin wannan Application ɗin akan wayarka kawai sai ka seta shi yarensa zuwa Yaren ka kana chat ɗin yana fassara maka da kansa kana gani kawai saikayi send.

Idan ka duba zaka ga wasu layi akan saman keyboard É—in wayarka guda uku a kwance kana dannasu zaka ga inda aka rubuta translation kawai sai ka danna akansa zaka ga ya nuna maka yare biyu kawai sai ka fara aiki.

Ga link É—in application É—in guda biyu

Application na farko

Download

Dounload

Application na biyu

Download

Download

Previous Post Next Post