Yanda zakayi Control din komai da wayar ka ( 2023 )



Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a wani sabon darasin. Yau darasin mu wani application ne da muka binciko a wannan sabuwar shekarar ta 2023 wanda ya kamata ku mallake su sannan kuyi amfani da su. Domin akwai abin mamaki acikin sa.



Hanya ce da zata baka damar ganin dukkanin abin da ke cikin wayar ka a TV din ka Ko Computer. Akwai tambayoyin da suka zo min akan irin wannan application din domin mutane suna so su kunna kallo a wayar su sannan suna ganin komai a TV din da kuma Computer su. 



Shi wannan application da zarar ka mallake shi a wayar ka to sai ka kunna tv din ka ko computer idan ka kunna zakayi share screen din wayar taka zuwa tv din ko computer.

Ta amfani da wannan application ne kawai zaka iya yin irin hakan. 

Da farko abin da zakayi bayan ka dakko application din wanda a chan kasa zan ajje muku link din sa sai kuyi install din sa.



bayan nan sai  ka bude shi wannan application din to zai baka damar hada ( Connect ) wifi da kuma Hotspot daga wayar ka zuwa TV din ko Computer. 

Bayan normal ka iya hada wifi ko nace Wireless bayan yayi connect to shkenn zakaga screen din wayar taka ya koma cikin TV din ko cikin computer taka.

Abin babu wahala kawai de nasan akwai wanda basu iya hada (Connect) din wireless a wayoyi ko nace da turanchi Device domin amfani da wani abuba ba.

To hanyar da zaka iya hada wireless da kuma hotspot shine.

Shi idan ka kunna hotspot to kaine zaka bayar zuwa dayar wayar. Idan kuma ka kunna wireless (wifi) shine zaka karba kenan.



Misali idan kana da wayoyi guda biyu kamar ta abokin ka da kuma wanda kake amfani da ita. Kuma kai wayar ka baka da Data wadda zakayi cht ko browsing amman abokin ka yana da Data a wayar sa. 

To sai ka amshi wayar abokin naka ka kunna Hotspot bayan ka kunna sai ka kunna wife (wireless) a wayar ka domin kine zaka amshi datar da zakayi amfani da ita a wayar taka.

To da zarar ka kunna application din hotspot din wayar ka zai kunna batare da ka kunna shi da kanka ba to sai ka kunna wireless  ( wifi) din computer ka ko na TV din.

Bayan ya gama connect sai ka dannan Screenmirroring. ko acreen Cast. shine wannan screen din zai fito acikin computer ko TV.

Wannan hanya ce mafi saukin gaske ya kamata ku mallaki application din.

Link din application din yana kasa zakuga na rubuta Download sai ku taba shine zai baka damar sauke application din a wayar ka.

👇👇👇👇

 Download

Previous Post Next Post