Yanda zakuyi Copy ( Dauka) komai a website ko App kyuta 2023

 Assalamu alaikum yan'uwa na ina muku barka da wannan lokachi. 

Yau zamuyi darasi ne akan wani application da ya kamata kusan da aikin sa sannan ku mallake shi. 

Suk da de bawani Jan darasin zanyi ba saboda application din babu wahala wajen amfani da shi. Sai de zan dan fada muku ayyukan sa.

Shin ko kunsan da yawa akwai website da kuma application ko wani socialmedia wanda idan kaga rubutu a jikin ko nace acikin sa kana buqatar kayi copy domin kayi amfani da wannan rubutun a wayar ka ko a wani waje ko ka turawa wani. Da yawa akwai website da kuma application da basa bayar da damar copy din rubutu domin kayi amfani da shi. Dole sai de ka karanta sannan ka barshi inda yake.

Nasan wasu gaba daya basu sani ba.

Sai de idan sunje daukar wani rubutu musamman Dalibai zasuga wannan rubutun yaqi Copy to sai su barshi suna ganin kamar laifin wayar su ne ko laifin service.

To ba laifin wani abuba bane sai laifin abinda kuka amfani da shi.

Hakan yasa na kawo mana wani application da zamuyi amfani da shi domin copy din duk wani rubutun da muke buqata.

Asalima idan ka buqachi kayi wannan copy din abin yaqi to sai kayi screenshoot din gurin sai ka shigo cikin wannan application da na baku. Shi wannan App din zai taimaka maku wajen daukar duk abinda yake a cikin wannan screeshoot din.

Na ajje muku link din application din a kasa sai kuje ku dakko shi domin amfani da shi.

Amman zan danyi qarin bayanin yanda ake amfani da shi kadan haka.

Nasan akwai masu buqatar sanin hakan.😒

Zan akje muku wani hoto wanda yake dauke da duk yanda zakayi amfani da wannan app a cikin wayoyin ku gashi nan a kasa

👇👇👇👇



Zaka dauki screenshot din gurin da kake so kayi amfani da shi kamar de yanda nayi muku bayani a baya.

kuma nasan kowa yasan yanda akeyin screenshot din.

bayan kayi screenshot sai ka tura wannan screenshot din zuwa cikin wannan application  To daman acikin app din akwai option da yawa sai ka zabi SELECT TEXT shine zai baka damar Gewaye iya inda rubutun da kake buqatar amfani da shi. 

Bayan nan sai ka dan Jara kadan shine zai baka copy din wannan abin ajikin Keyboard din wayar ka wanda zaka iya zuwa duk inda kake so kayi paste dinshi. ko kuma Direct daga cikin app din sai kayi share din sa.

Akwai app da yawa ko social media ko browser din da basa ba da damar copy. Wani lokachin ma Facebook baya ba da damar copy din Text amman ya danganta da wayar ka.

Ga link din application din a kasa zakuga na Rubuta Download da koren rubutu sai ku taba shine zaku sauke app din a wayoyin ku

👇👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post