Ga duk mai chat a whatsapp ya wani app a wannan shekarar 2023

 Assalamu alaikum! Yan'uwa ina wuni 

Yau wani Application na kawo mana mai matuqar amfani domin ya bada abubuwa da yawan gaske wanda zaka ita amfani da shi.

Wato shi wannan application ne da zai bada abubuwan da baka taba mallaka acikin wayar ka ba.

Application ne da ya danganchi yanda zaka kawata chat din ka na whatsapp saboda duk abubuwan dake ciki ya danganchi whatsapp.

Wajen abubuwa 7 ko sama da haka.😊

Kamar de yanda kuka ga bayanin acikin video. To amman nayi bayani ne akan application na iphone acikin videon kenan.

Sannan shi dayan application din na bangaren android da banyi bayanin sa a acikin videon ma shi kusan duk aikin su daya.

Sai de acikin na iphone akwai abinda babu haka acikin na android akwai abinda babu.

Shi yasa muke dan rubuta muku dan bayanin da bamuyi acikin videon ba.

Amman dukkanin su zan ajje muku link din su a kasa sai kuje ku mallake su.

Kafin nan kowane application zan dan zayyana muku abubuwan da ya kunsa.

       APPLICATION NA IPHONE

Wato shi wannan application din idan ka bude shi a wayar ka ta iphone zai baka damar abubuwa kamar haka a whatsapp chat din ka domin kawata chatting din ka ga abokai da yan'uwa sannan da masoya.

1) Abu na farko shine zaka iya hada whatsapp biyu a wayar ka ta iphone. Misali zaka iya saka duk chat din matar ka ko budurwar ka ko kuma idan kana da kanwa haka. Domin zakayi amfani da wajen Qrcode ne.

2) Akwai direct message wato idan bakayi save din number mutum ba ta whatsapp to idan ka shiga gida na biyu zaka iya turawa kowace number sako batare da ka save din number a wayar ka ba.

3) Bugu da qari akwai private browser domin yin browsing ko zaka ziyarchi wani website sannan kana tsoron kada a dauki bayanan ka. To idan kayi amfani da wannan Private browser ta acikin wannan application din baka da matsala ta wannan fannin.

4) Akwai wajen ajje hotuna domin biye sirrin ka wanda babu wanda zai bude ma ballantana yaga abin da ka zuba aciki. Da zarar ka bude wannan fanni kawai zai baka damar saka duk wasu hotuna da kake so ka boye sannan zaka iya sakawa wannan fannin password babu wanda zai bude sai kai.

5) Akwai bangaren da zaka rage ko ka saita hoton da kake so ka saka a DP din ka na whatsapp. Wani lokachin kana buqatar kaga ka saka wani hoto amman saboda ba girman DP din bane bazai shiga ba.

6) Akwai bangaren wasu da EMOJI😉 wato irin wannan abin👉( 🥸😒🥲❤️😂😄😎🏃🫡) zaka iya rubuta sunan ka ko wata kalma ko sunan budurwar ka sai kayi generate da irin kowane emoji da kake so ka hada domin burge wanda kuka chat da shi.

7) Sai kuma uwa uba bangaren chanja kalar rubutu wanda shi idan ka shiga wannan bangaren zakaga akwai bangarori acikin sa shima. Zaka zayyana kowane rubutu da kakeson turawa abokin chat din ka musamman masoya😍❤️.

Wannan kadan daga cikin Application na iphone din da nayi video akai.


      APPLICATION NA ANDROID

Wannan application na wayar android yasha banban da irin na android.

Shi a gurguje zai dan fda muku kadan daga cikin sa

Shi ta cikin sa zaka iya save din status batare da kayi amfani da whatsapp gb ba.

Akwai fake chat idan kana so ka zolayi wani da shi.

Ga dai abubuwan da ya kunsa nan a cikin hoton da na ajje a kasa.

👇👇👇👇


Sannan duk mafi yawanchin abin da na iphone yana dashi shima wannan yana da shi.

A kasa zaku ga na rubuta Android App da kuma iphone App kowane sai ku tavab ku sauke a wayoyin ku

Nagode

Iphone App

Android App

Previous Post Next Post