Gano matsalar waya kowace kala ce





Assalamu alaikum barkan mu sake saduwa a yau a wani sabon darasin!.

Yan'uwa yau wani darasi ne akan bangaren waya kowace kala ce wato Android da kuma iphone.

Yanda zaka gne duk wata matsala ta waya wadda take hannun ka ko wadda zaka siya koda sabuwa ce.

Kamar yanda kuka ga cikakken videon a youtube da kuma page dina na facebook. Nayi bayani akan abu biyu Application da kuma website.

To shi application din duka na wayoyin biyu ne shi yasa ma a kasa idan kukaje zaku ga kowace waya na ajje mata application din ta.

Sai de shi website din yana amfani ne bangaren iphons zaka gane koda wayar ma ta sata ce ko ana tracking din ta gaba daya.

Duba da yanda muke samun mabiya  a kowane lokachin da kuma shafikan mu kala davan-daban zan danyi bayani koda ba kowa bane ya ga videon darasin.

Application din da na ajje muku shi amfanin sa zaka saka shi a cikin wayar taka android din ko iphone din bayan ka saka shi shine zai baka damar binciko duk matsalar wayar.



Abinda ya danganchi Ram din ta ko GB din ta da kuma duk wani bangare na hardware din wayar.

Inde ka mallaki application din sannan kayi bincike akan sa zaka gane komai da ya kakata ka sani akan waya.

Zakagane yanda karfin battery koda zai rike chaji ko bazai rike ba.

Zaka gane karfin network din wayar kowane kala ne.



Zaka bi gida daya bayan daya kana dubawa na duk wani bangarori na wayar da take a hannun ka.

Sai de kuma shi wannan application din bazaka iya duba sabuwa wadda take acikin kwali ba. Sai de scondhand wadda ka siya ko aka siyar ma ko dan'uwan ka ya siya zaku iya dubawa idan kuka saka application din acikin wayar.



Idan kaje kasa zakaga Android app da kuma iphone app dukkanin su sa koren rubutu to idan ka taba na android shi masu amfani da Android ne zasu sauke shi acikin wayoyin su.

Amman idan ka taba iphone App shi kuma masu amfani da iphone ne zasu saka shi acikin wayoyin su.

Sannan kafin nan sai magana akan website din da zan ajje muku shi a kasa.

Shi kuma na masu amfani da iphone ne zaka gane duk wata matsala ta iphone yaushe aka fara anfani da ita sannanshin ana tracking din wayar ko kuma wayar akwai icloud acikin ta. Da duk wata matsalar da ya kamara ka sani akan wayar da ka siya.

Sannan koda sabuwar waya ce tana cikin kwalin ta baka bude ba  Zakayi amfani da IMEI na wayar komkuma serial number na wayar. Shi zaka shiga cikin website din sai ka saka wannan IMSI ko Serial din shine website din zai fada ma gaskiya akan wayar.

Idan sabuwar waya ce ajikin kwalin zaka nemo wadannan abubuwan da na lissafa wato IMEI da kuma Serial no.

Idan kuma normal wayar ba acikin kwali take ba idan zaka nemo imei no na wayar zaka dannan *#06# shine imei din zai fito sai ka shiga wannan website din idan kuma seria number zaka nemo na wayar zaka shiga cikin aetting bayan nan sai ka nemo General bayan nan zakaga About sai ka taba bayan ka taba sainkaje kasa zakaga Serial number sai ka dauka kaje cikin wannan website din.

Bayan ka  rubuta zai fadama komai akan wayar koda ma an fara anfani da itane. 

A kasa zakaga na rubuta Website sai ka taba shine site din zai bude ma.

Wato darasin nan yana da amfani sosai kwarai da gaske.

Ga link din nan

👇👇👇👇

 Android app

Iphone App

Website

Previous Post Next Post