Sabon Application Clipboard. Zai saukaka ma chattin din ka 😍 2023

Assalamu alaikum barkan mu da warhaka ina fatan kuna lafiya.

Yau darasin mu akan wani muhimmin application ne wanda ya kamata ku mallake shi.

Domin zai baki damar copy din rubutu duk adadin da kuke so batare da kunsha wahala ba.

Wato nasan wani zai ce bai fahimchi bayanin nawa ba.

To ku biyo mu a sannu a hankali zanyi muku bayani dalla dalla insha Allah.



Idan kaga wani rubutu a wayar ka koda ace number waya ce ko hoto ko kuma wani bayani. To idan kana so kayi amfani da shi dole sai kayi copy sannan sai kaje inda kake so sai kayi paste dinshi a inda kake so. Sannan idan kanaso ka qarayin wani copy din to wancan na farko dole zai goge sai de na biyun wanda kayi copy.

To shi amfanin wannan application din zai baka damar copy din duk adadin rubutun da kake so batare da ya goge ma na farko ba.

Kuma zai maqale ma ne a jikin Keyboard din rubutun ka ba.



Koda kana da numbobi da yawa kuma kana so kayi copy dinsu sannan kayi amfani da su a wani application ko chatting haka. Normal ta hanyar amfani da wannan application din zaka iya copy din duk abinda kake so sannan duk yawan su. Koda sunsha bambam.

Qarin bayani akan haka.

Misali a cikin wayar ka kana rubuta littafi na arabic da hausa da kuma wani yaren kamar eng kamar de yare Goma haka.

To kana da MS Word na rubutu wanda kake rubuta littafin naka to su kuma sauran yarikan kana dakkowa ne a wani guri kamar online haka ( Google ). To idan kayi Search din Arabic sannan kayi copy din abinda ya danganchi Arabic din to zai sauka ajikin keyboard din ka. Sannan batare da kayi paste din shi a MS Word din da kake aiki ba Zakaniya copy din dukkanin yarikan naka. Wanda kake so kayi amfani da shi.

Batare da wani ya goge wani ba. Zai jera ma a jikin keyboard din sannan koda kaje MSword din dukkanin su idan kazo daidai inda kake so kayi amfani da kowane yare kawai taba kan rubutun zakayi zai sauka inda kake so ka ajje shi.

Ga de link din application din a kasa sai ku taba ku sauke a wayoyin ku sannan babu wata wahala wajen amfani da shi.

Kawai kana budewa app din zai bude ma babu wata wahala aciki. Sannan bashi da wani nauyi koda kana tsoron ya cike ma kan wayar taka.

Ga link nan a kasa zakaga an dubuta Download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.

👇👇👇👇👇

 Download

Previous Post Next Post