Sabon Application na kasuwanchi 2023

 Assalamu alaikum! Ina fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Yau videon mu ko nace darasin mu akan kasuwanchi ne. Sannan kasuwanchin ma ba kalle sai kana da babban kasuwanchi ko trader ba.

Application ne da zai taimaka ma kasan adadin lissafin gaba daya kayayyakin ka da kuma nawa ka zuba a shago bugu da qari da rubuta dukkanin invoice idan ka siyarwa da wani ko wasu kaya sannan zaka iya tura musu ta normal message ko gmail ko whatsapp ko kuma kayi print din sa a matsayin hardcopy kamar yanda manyan shaguna sukeyi sannan ka bawa mutum a hannu.



Wannan application din batare da ka mallaki computer ko wata software mai tsada ba. 

Da zarar ka mallaki wannan application zai baka damar iya saita kasuwanchin ka!. Nawa ka siyar da kaya da kuma kudin da kullum suke fita da nawa kake yi duk kullum da nawa ne acikin shagon. Kamar de wata computer da manyan shaguna suke amfani da su.

Maganar gaskiya wannan application yana da amfani sosai wallahi. 

Saboda akwai wanda bai iya lissafin shago ba abubuwa sunyi masa yawa kuma koda yayi rubutu a littafi bazai zo masa yanda yake so ba.

Amman shi wannan application cikin burgewa zai baka damar saita duk wani fanni na kasuwan chin ka. 

Zaka iya banbance bangarorin ( Yan bashi ko kuma nawa ake binka ko nawa kayi yau ko jiya sannan nawa ne cash a hannun ka da kuma gaba daya kayan da yake shagon ka da wanne da wanne ne ya rage ).



Ka bi a hankali application din bashi da wahala sosai da kanka zaka iya saitawa.

Sannan zai saukaka ma abubuwan ka normal ba sai kayi amfani da computer ba.

Koda ma a shagon ka akwai computer to zaka iya amfani da wannan application din a wayar ka. 

Ka dinga lissafa shagon ka ko kayan ka.

Link din application din yana kasa zakaga na rubuta Download da koren rubutu sai ka taba shine zai baka damar sauke application din a wayar ka.

👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post