Wannan Application din Zai tabbatar ma baka iya karanta FATIHA ba😭😭

Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu.

Bayan sallama irin ta addinin muslunchi hakan yasa na kawo mana abinda ya danganchi addinin mu sannan maganar ko zancen mahaliccin mu. Wato ( Alqur'an).

Duk abinda akeyi idan akace abinda ya danganchi addini ne sannan zai taimaki rayuwar ka duniya da lahira to ya kamata ka mayar da abin da muhimmanchin gaske.

Dole nayi shimfida kafin ma na sanar da ku da me nazo yau.!

Application ne na qur'ani wanda zai baka damar koya ma duk wata aya ko surah ko shafin da kake tunanin ka iya karantawa.



Da yawa muna kuskure wajen karanta wani bangare na qur'ani amman saboda wasu dan abubuwa shi yasa bama iya zuwa gaban wanda suka iya su koya mana.

To ni a ganina wannan sauki ka samu saboda kana gida a zaune zaka koyi surah ko aya da kuma yanda ake karantawa.



Wallahi tallahi duk sallah da kake idan fatihar ka ba daidai kake karantawa ba to akwai gyara akan sallar.

Da farko bayan ka bude application din zai baka damar zabar shin ka iya karanta wani fanni na qur'ani ko kuma baka iya karantawa ba.



Idan ka iya zai fara ma da Suratul qul'huwallahu Ahad wato ( IKHLASI ).

Kuma karantawa zakayi yana jin ka idan ka karanta ba daidai ba zai dakatar da kai da wata alama domin wayar ka zatayi qara sosai sannan zai baka damar ka duba inda ka karanta ba daidai ba. Shine application din zai baka damar sauraron wani daga cikin malaman qur'ani dan ya karanta ma daidai har sai ka gyara.



Shin zai baka damar taba continue.

Amman daman tun farko idan baka iya karantawa ba a kasa zaka ga ican't recite right now. Sai ka taba shine direcf yasan baka iya karantawa ba.

Zai bude ma.

Bayan ya budema zai fara da suratul fatiha.

Amman zaka iya zabar surah ko izfi ko Juz.

Zaka karanta. 

Amman ga video nan a kasa nayi cikakken videon darasin sai ka taba ka kalla.

👇👇👇👇👇


Akwai challenges da zaka shiga idan kana kullum yanda zakayi karatun.



A takaice de ga link din application din na duka wayoyin guda biyu.

Iphone da kuma Android.

A kasa zakaga Android App da koren rubutu shine na wayar Android sai ka taba ka sauke application din.

A kasan sa kuma zakaga iphone App shi kuma na masu amfani da wayar iphone ne sai ku sauke su a wayoyin ku.

Bayanin a rubuce bazaiyiyu ba saboda abin dole sai acikin video.

Duk da nasan kun kalli videon a youtube da kuma facebook page sannan acikin wannan rubutun ma na ajje muku shi sai ku kalla.

Kada ku manta da share din videon zuwa ga yan'uwa Nagode


👇👇👇👇👇

 Android App

Iphone App

Previous Post Next Post