Yanda ake hada IV ko sticker ka sami kudi

 Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa a sabon darasin mu!.

Yan'uwa yau application din namu mai tsadar gaske ne wanda ya kamata ace ka mallake shi sannan kayi aiki da shi.

Saboda zaka iya hada duk wata kalar edting na hoto irin su poster,flyer,Invitation,sticker. A kyuta sannan ka sami kudi da shi.

Kuma abinda zai baka sha'awa da wannan application din shine.

babu wahala wajen yin aikin idan zaka hada wani iv ko poster

Domin da zarar ka bude application din zai fitoma da kala kalan design na editing kawai idan ka zabi wanda yayi ma shine zaka zaba kana zaba sai ka cire duk wani abu da kake so ka chanja.

Kuma koda akwai hoto ajikin abinda ka zaba. Zaka iya cire hoton jiki sai ka saka wanda kake so ka hada editing!.

Wato wannan application yana da kyu sosai na tabbata akwai wadanda suna so suga kala kalan design me kyu.

Bayan nan koda ka bude application din sannan baka ga irin design din da kake so ba. A sama zakaga wajen Search sai ka rubuta irin abinda kake so ka hada. Misali Idan invitation ne sai ka rubuta idan Engagement ko birthday ne shima sai ka rubuta to iya abinda ya danganchi abinda kake so shine zai kawo ma.

Ga ire-iren misalan abubuwan da na hada da irin wannan application.



Akwai su da yawan gaske amman iya wannan zan nuna muku!.

Zaka hada abinda mutane da yawa zasuyi tunanin a computer aka hada abin.

Saboda ko logon app din bazai fito ba.

Illa iyaka idan kana son amfani da wani abu mai muhimmanchi aciki to shne zasu buqachi kayi upgrade din app din.

Dukka de zan ajje muku link din application din a kasa.

Na dukkanin wayoyin iphone da kuma android. Zakaga iphone App shine na wayar iphone. Haka kuma na wayar Android zakuga na rubuta Android App.

👇👇👇👇🏃

iphone App

Android App

Previous Post Next Post