Yanda zaka dawo da hoto ko videon da k gohe a wayar ka ko memory.

Yanda zaka dawo da hoto ko videon da k gohe a wayar ka ko memory.



Assalmu alaikum barkan mu da sake kasancewa damu a wani sabon darasin. Yan'uwa yau darasin mu yana da amfani kuma amdade ana buqatar wannan darasi ko wannan hanyar.

Hanya ce da zaka dawo da duk wani abu da ka taba gogewa a wayar ka ko memory ko flash. Abinda yasa nace haka saboda idan normal abin a wayar ka ne zakayi amfani da wannan application acikin wayar da abin ya faru. Amman abinda ya danganchi memory ko flash ko wani devices daban to zakayi amfani da software ta computer ce amman dukkanin su sunan su daya da Application na waya da kuma software ta computer din.

Amman yanzu zanyi bayani ne akan application saboda akan sa ne nayi videon kamar yanda kuka kalla a page dina na facebook. 

Sannan ga wanda bai kalli videon ba zan ajje muku shi a kasan wannan rubutun kawai sai ka taba ka kalli yanda akw saita application din.

Da dama mukan rasa wani abu namu mai mahimmanchi ko ka goge ko kuma ka neme shi acikin wayar ka ka rasa shi. 

Sannan kowace kalar waya ce. Ina nufin koda karama ce inda Android ce.


Akwai application kala daban-daban mai irin wannan to amman shi wannan wanda na kawo muku ya sha banban da kowane kalar application wanda zaka iya dawo da duk abinda ka taba rasawa a wayar ka.

Ga wadan da basu sami damar kallon videon ba zan danyi musu qarin bayani kadan.

Da zarar ka bude application din acikin wayar ka zakaga yanayin search wani lokachin kuma zai tambaye ka me kake so ka dawo da shi. Waka ce ko video ko hoto.


kana zaba zaiyi ma search ko ince ya binciko ma su kamar haka.


To amman bayan sun gama dawowa sai kui mark din su. Misali kowane sai ka taba shi ko kuma akwai select all.

Sai taba idan gaba daya kake somka dawo da shi din.

Bayan ka gama a sama zakaga wata alamar save kamar alamar memory a tsakanin alamar setting da wasu Dogo guda uku.

Idan ka taba man shine zai tambaye ka a me kake so kayi save din wannan abubuwan naka.

Saboda asali idan ka gansu anan bawai sun zauna akan wayar ka bane.

Sai kayi yanda na ce a baya sannan zai ajje ma a kan wayar taka ko

memory kode Drive ko duk inda kake so ka ajje shi.


To wannan hanya ce mafi daukin da zaka iya dawowa da duk abinda ka taba gogewa a wayar ka hoto ko video ko waka.

Ga link din application din a kasa sai ka taba shine zaka sauke application din a wayar ka.

Download

Ga videon nan a kasa ga wanda yakeson yaga yanda ake saita application din

👇👇👇👇👇



Previous Post Next Post