Yanda zaka mayar da komai zuwa cikin wayar ka 2023

Assalamu alaikum barkan mu da warhaka ya sanyi kuma da kuma fama da wannan yanayi na rashin Cash a hannu🥲. Abin ba dadi sam Amman ya kamata mu danyi kokarin ganin cewa muma mun fara amfani da banki ko wani wallet domin amfanin yau da kullum. Allah yasa mudace ameen.

Yan'uwa darasin mu na yau akan wani application ne da zai baka damar mayar da dukkanin hoto ko paper ko idcard ya koma cikin waya.




Wannan hausar da nayi nasan wasu basu gane ba gaba daya.

Amman zan danyi kokarin fahimtar da ku insha Allah.

Akwai lokachin da zak tsinchi kanka akan cewa kana so ka turo wani certificate naka na makaranta ko wata takarda a online to zaka rasa yanda zakayi domin koda ace kana neman wani aiki ko kuma wata makaranta zasu iya baka qa'idar dole sai de ka tura su a matsayi pdf. Wato acikin waya kenan batare da ka tura a matsayin wannan hoton da ka dauka ba.

Ko kuma yan makaranta wanda suna da wani handout amman wannan handout din yana da yawan gaske babu damar kabi daya bayan daya kana daukar sa a matsayin hoto. To shi wannan application din zai mayar ma dukkanin wata paper ta koma kamar a cikin waya aka rubuta ta.




Koda idcard idan wata ma'aikata ta bukachi ka tura da shi. Ko kuma already kana da wani pdf wanda ake so ajikin sa ka hada da hoton ka ko takardun ka ko idcard din. To kaga ba damar ka dauki hoton wadannan abubuwan sannan ka hada shi da wannan abinda ake so ka tura a tare. To shi wannan application din zai baka damar mayar da dukkanin decument dinka ya koma pdf din normal. Bayan kuma ka gama scan din zaka iya gyara rubutun ta cikin wayar ka.

Wani lokachin kuma ga masu rubutun litattafai bangaren boki ko arabic duka koda wane irin rubutu ne. To zakaga akwai rubutun da dadewa an riga an buga su. To acikin wadannan littattafan kana so ka dauki wani abu to kuma zakaga wannan littafin ba acikin wayar ka yake ba kuma rubutun naka acikin wayar naka kake rubutawa. To zaka iya amfani da wannan application din kayi scan din duk gabar da kake so acikin littafin da kake so ka saka wani hadisi ko wata maganar.

Bugu da qari shine wani lokachin ma zakaga kayi rubutun a paper amman idan zaka tura ba lalle a gane rubutun naka ba. 



To idan kayi amfani da wannan application din zai iya scan din wannan rubutun normal ya koma kamar wannan rubutun da kake karantawa.

Ya kamata ku mallaki wannan application a cikin wayoyin ku!.

Zan ajje muku link din application din a kasa. Zakuga na rubuta Download din sai ku taba shine zaku sauke application din acikin wayoyin ku.

👇👇👇👇👇👇


 Download

Previous Post Next Post