yanda zakayi Kiran waya kyuta ( Prank ) 2023

 Assalamu alaikum barkan mu da warhaka. Ina fatan kowa yana nan lafiya lau. Yan'uwa kwana biyu kun dan jini shiru ko😄. To yanayi ne na aikin yau da kullum kawai de addua zakuyi mana muda iyayen mu da kuma gafara zuwa mahaifina wanda ya dade da rasuwa. Nagode



Yau darasin mu kusan zan iya cewa na manyan yara ne😄 Amman duk da nasan akwai masu buqatar irin wannan application.

Application ne da zai baka damar wani ya kira ka a kyuta ko nace da turanchi free.

Nasan wani baigane me nake nufi ba. Amman zanyi bayani daya bayan daya har ku fahimta.

Da yawa akwai masu buqatar idan sunje wani guri suna daga wayar su domin wani ko yan gurin su san wane irin waya ce a hannun sa.

To wani sai de ya hada baki da wani abokin sa da zarar lokachin yayi sai ya dinga kiran sa a waya.

To kaga ai wannan hanyar akwai wahala sosai sannan akwai matsalar network.

To shi wannan application zai baka damar saitawa da lokachi da rana da kuma adadin kiran da kake buqata shi application din ya diga koran ka a lokachin.

Sannan zaka iya rubuta Number da suna wanda babu wanda zai gane wannan kiran da akeyi maka na karya ne.

Bugu da qari zak iya daga wayar sannan za'aga time ko scond na waya yana tafiya har sai ka gaji da yin wayar.

Bayan nan zaka iya zolayan budurwar ka ko abokin ka da wannan application.

Shi wannan applocation na koya muku ne domin ilmi da kuma masu buqatar amfani da shi.

Saboda haka shi wannan application yana da sauki wajen saitawa kawai kana bude application din zakaga alamar (+) idan ka taba zai baka damar saitawa lokachi da rana da kuma number da suna gaba daya.


Bugu da qari zaka iya record din irin wayar ma da kake so kayi da wannan number.

Misali idan ka taba wajen Add voice kamar yanda kuka gani a jikin hoton da na dora a sama. Zaka iya tsara record din da idan shi app din ya kira ka kuma ka daga kawai app din zai kunna wannan record din wanda tun asali ka saita shi.

Kaga koda idan ka taba ko ka daga kiran za'a ji magana tanayi da kuma scond na tafiyar kiran babu wanda zai gane wannan kiran na karya ne.

Zaka iya zabar irin screen din kowace waya idan an kira ka.



Sannan zaka iya saita lokachi na kira kamar de yanda kuka ga gaba daya acikin hoton daga dora muku.

Saboda haka ku mallaki wannan application.

Kaje kasa zakaga na rubuta dowload da koren rubutu sai ka taba shine zaka sauke application din a wayar ka.

👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post