No title

 Assalamu alaikum barkan mu da warhaka. Ya kuma dan zafin da ya tunkaro mu. Allah yasa mu wuce lafiya ameen.

Wato Yan'uwa wani application ne mai amfani sosai. Domin ganin cewa ya nuna ma asalin duk hanyar da kake buqata kaje wani gari ko unguwa.



Musamman na wannan lokachin da muka shiga da hakin tsoro domin gudun kada a sami matsala idan zakaje unguwa ko gaba daya zaka bat garin ku kaje wani gari haka.

Shi amfanin wannan application din zayyi maka rakiya duk inda zakaje. Da zarar ka rubutu sunan garin ko unguwar to tun daga inda kake zai dinga nuna maka hanya har gidan ko garin da kake so kaje.


 Da zarar ka rubutu sunan inda zakaje misali kana Kano sai ka rubuta Jigawa ko Abuja da kuma sunan unguwar da zakaje a wannan garin to tun daga kano zai dinga nuna maka hanya har ya kawo ka inda zakaje.

Abu daya anan zakayi shine ka tambayi sunan unguwar da zakaje to idan aka fada maka sai ka rubuta a cikin wannan application din to shi zai kawo ka har unguwar da ka rubuta. Ko kuma ma tun farko an turo ma da link din location din inda zakaje kamar yanda na taba nuna muku a wani video na yanda ake tura location. To ta wannan location din zakaga asalin unguwar da kake buqata kaje shine application din idan ka bude kuma ka rubuta sunan unguwar ko garin ko duk inda de zakaje. 

Zakaga almar Kibiya ( Arrow ) har gurin da kake buqata kaje din.

Sannan koda ma a cikin garin da kike ne shima zai iya yi maka rakayi har gurin da kake buqatar kaje.

Nasan da yawan ku kunsan Google Map to duk yanda zakayi amfani da Google map haka shima wannan yake. Sai de wani lokachin zaka iya siyan Waya amman bata da google map ko gaba daya ma baza ta dauki google map din ba kamar irin wayoyin da muke siyowa. Wato london use.

Zakuga gaba daya basa daukar duk wani application da ya danganchi Google.

To idan ka mallaki wannan application din komai zai zo ma da sauki wajen tafiye-tafiye.

Batare da kana tsoron inda zakaje ba saboda gudun kada kayi tambaya a sami matsala. Bakasan ko su wa zaka tambaya ba Allah ya kiyaye.

Sannan koda zaka tambaya kana tsoron ba irin yaren ka bane. Zaka iya amfani da wannan application sai kayi record din maganar ka. Shi application din zai baka damar chanja yaren ka zuwa wanda zaka tambaya.

Haka shima idan zaiyi magana sai ka ya fadawa application din shine zai fassara ma zuwa yaren ka.


Ga link din application din a kasa sai ka taba ka sauke acikin wayar ka. Zakaga na rubuta Dowload da koren rubutu kana tabawa shine zaka sauke a wayar ka.

Download

Previous Post Next Post