Yanda zakayi control din wayar budurwar ka ko 'ya'yan ka Ka hana su hawa Tiktok😍

Assalamu alaikum barkan mu da sake saduwa a sabon darasin mu na yau akan wani application ne da zai baka damar control din wayar yayan ka ko matar ka ko budurwar ka ko kuma wayar ka gaba daya.



 Shi wannan application amfanin sa shine zaka iya saita adadin da kowane application za'a yi amfani da shi.

 BADA HAKURI

Ina mai bada hakuri saboda a videon nace zan baku application guda biyu kowane yana da amfanin sa.

 To amman wannan application guda daya dukkanin abinda na fada a cikin videon shi kadai zaiyi maka.

Kamar yanda kuka san kullum burin mu mu kawo muku duk wata hanya mafi sauki domin amfani da shi a wayar ka da sauran su.

Kamar yanda kuka ji bayani acikin videon.

Akwai hanyar da zaka gane adadin da mutum yake amfani da duk wani application a wayar sa. Duk sati ko duk wata ko duk wani lokachi na Awa ko minti.

Sannan zai baka damar kulle duk wani application ka bada lokachi daga wannan lokachi zuwa wannan lokachi.

In har ka saita to idan lokachin da ka saita baiyi ba kwata-kwata application din bazaiyi amfani ba gaba daya.

Misali: Idan ka zabi application na Tiktok ko whatsapp daga karfe 10PM na dare zuwa 8Am Na safe. To a Dan wannan lokachin kwata kwata application din idan aka bude shi bazaiyi ba. Zai nuna ma akan ko ya sami matsala.

Sannan zaka iya rubuta dan wani message da idan anyi kokarin bude application din shi wannan app din zai nuna. 



Misali: Zaka iya rubuta ( Ina kallon ka/ki ki kwanta kiyi bacchi.). Ko kuma wani sako wanda zaka razana dan naka ko budurwar ka kanwar taka.

 Tabbas wannan application din yana da amfani da abin mamaki.

Amfanin application din na biyu shine zaka gane duk wani application da aka fi amfani acikin wayar.

Sannan amfanin wannan na biyun shine. Idan ka tashi kashe ko kulle application din to zaka rasa wanda zaka kulle saboda zakaga akwai chat da yawa a wayar dan naka kommatar taka ko kanwar taka.

Idan kayi amfani da wannan hanyar zaka binciko wani chat ko application dan naka yafi amfani da shi a wayar tasa. 



To anan zaka ga jerin dukkanin Application da yake a cikin wayaar. Sannan zakaniya taba daya bayan daya kaga lokutan da aka fi budewa da kuma adadin dadewar da kake yi a akai.

Da zarar ka ga application din da yaron yafi amfani da shi to shine zaka bi hanya ta farko da na baka.

Sai ka saita ka kulle shi lokachi bayan lokachi shine zai dingayi.

Amfanin wannan darasin shine akwai yaran da zakaga koda a makaranta ko lokachin aiki ko wani lokachi da baka so suna amfani da wani chat ko application ko wane kala.

Zaka iya kashe shi babu tanda zaiyi ya gane hanyar da zai bude.

Bayan ka gama amfani da application din ko nace ka saita sai ka bi hanyar da ake boye application din saboda kada wanda ka sakawa a wayar sa yaga wani sabon application.

Domin idan yaga wani sabon application din zai iya cire shi kaga zai bata abinda ka saita sai de ka qara amsar wayar ka qara saitawa.

Duk de ga link din application din a ksa zakaga na rubuta Download da koren rubutu sai ka taba bayan ka sauke application din sai ka tura a wayar da kake so kayi amfani da shi.

Nagode

👇👇👇👇👇

 Download

Previous Post Next Post