(SIRRI ) Yanda zaka gaa Hoton wanda ya tabama waya bayan ka saka Chaji ko ka ajje. 2023

Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachin. Yau darasin mu akan wani application ne da yake da amfani sosai saboda zai baka damar gane duk wanda ya tabama waya koda Barawo ne.

 Wannan application din koda ka ajje waya idan aka kokarin daukar ma wayar sannan aka saka password na wayar zai dauki hoton wanda ya dauki wayar koda barawo ne ko matar ka ko yayan ka.

Abin da yasa na lissafa mutanen harda iyalai shine. Koda duk wanda ya dauki wayar ya kokarin saka password din wayar taka zai dauki hoton sa.

 Zakaga duk wani password da ka saka a wayar ka to idan kana da mata ko yaya suna kokarin sanin wannan password din idan ka ajje wayar ka koda ajikin chaji ne ko kuma idan ka ajje to akan samu wanda zai dauki wayar taka. Kuma idan kayi magana akan wanda ya taba ma wayar zakaga an wi fafama gaskiya.



To wannan application shine zai tabbatar ma da wanda ya dauki wayar taka saboda harda hoton sa ma.

 Na ajje link din application din a kasa sai ka taba ka dakko shi ka saka a wayar ka.

 Abin mamaki da wannan application din shine bashi da wahala wajen saitawa.

Sannan koda kaine kayi mistake din saka password ba daidai ba to wayar taka zata dauki hoton ka sannan ta ajje ma a gmail din ka ko acikin application din naka.

 Idan ka shiga akwai folder da yake ajje ma dukkanin hotunan duk adadin su. Sai de idan kaine ka goge da kanka.

 Akwai abin burgewa sosai😍.



Kawai kana dakko application din zakaga Continue da sauran su. Sannan a karshe zai baka damar saka application din a matsayin device admin shi kuma ba wani wahala bane kawai zaka bi duk hanyoyin da application din ya buqata.

 Sannan zai iya baka damar saka Gmail din ka domun ya dinga tura ma hotunan ta Gmail din naka.

A kasa zaka ga an rubuta Download da koren rubutu idan ka taba shine zai baka damar saukewa a wayar taka.

👇👇👇👇👇👇

 Download

Previous Post Next Post