Wannan application din babu kakar sa a shekarar nan 2023// photomath😍

 


Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi ina fatan kowa yana cikin koshin lafiya.

Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne na lissafi kowane kala.

Zai solving da hausa zai fitar ma da duk wata math lissafi kenan idan kana buqata koda ace a jikin takarda yake zaka iya scanning din wannan questions din ta cikin application din.

Sannan zai fitar ma da amsar daidai.

Da yawa akwai hanyoyin da suka fito na samun sauki sai de bamu san su ba irin hakan ne yake sawa muke gaddama da wanda ya bamu labaran irin wadannan application masu fasaha.

 Zai taimaka maka ya fitar ma da duk wani kalan lissafi wanda kake buqata sannan zai baka damar rubutawa ma acikin application din sannan zaiyi ma solving din sa.

 Wato duk bayanan da nakeyi nafi lura da wadanda sukeyin school a halin yanzu. Saboda sauki ne yazo koda malami ya baku assignment kowane kalar lissafi to wannan application din batare da kunsha wahala ba kawai zaka dauki quetions din a ka rubuta a jikin takardar ta cikin application din.

Nan take zai fitar ma da amsar ka kawai dauka zakayi ka rubuta a cikin littafin ka.



 Akwai hanyoyin da zaka iya koyar duk wani salo na math ( lissafi ) ta cikin wannan application din kuma ta hanya mai saukin gaske.

 Daya bayan daya zai dinga kowama inde kabi duk wani hanya da yake nuna maka.

 Kawai de a takaice wannan application ne na lissafi kowane kalar lissafi kuma.


 Ina wadanda suke ganin lissafi yana da wahala wajen ganewa?. 

Da zarar ka mallaki wannan application din cikin ikon Allah zaka iya komai da kake buqata. Kuma idan ka tashi koya zakaga hanya ce mafi sauki zai bi domin ya koyar da kai kowane kalar lissafi.


 Kuma gaba daya application din wajen amfani da shi babu wata wahala saboda kawai kana bude application din zakaga babu wasu abubuwan wuya kawai menu ne da kuma camera.

 Ga link din application a kasa na ajje muku zaku ga na rubuta Download da koren rubutu da zarar ka taba shine application din zai sauka akan wayar ka.

👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post