Wannan Application din zai qawata ma Fuskar wayar ka 2023

 Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi. Yau darasin mu akan wani qawataccen application ne wanda zai qawata wayar ka ta android ya kamata ku mallaki wannan application din.



Duba da irin abubuwan da muke sakawa a waya na Launcher ko wallpaper zakaga gaba daya wayar taka bata da wani kyu.

Sannan nasan akwai wanda yake amfani da launcher a wayar su ko su dora hoton wani mutumin ko mace ko na campany kawai da fuskar wayar taka tayi kyu.

To shi wannan application ba launcher bace. Kawai wallpaper ce masu kyu da inganchi sosai. Wanda zaka qawata fuskar wayar ku.

Sannan koda ace akwai launcher da ka dora akan wayar taka zaka iya amfani da wannan application na wallpaper.




Akwai banbanchin Launcher da irin wannan application din.

Launcher idan ka dora akan wayar ka zata chanja ma gaba daya wayar taka. Abinda ya danganchi Menu ko Home ko Rubutu da yake akan wayar taka ta asali.

To shi wannan application ba na launcher bane kawai na Wallpaper ne wanda zaka dinga dora hotuna masu qawatar wa. Batare da kayi amfani da wani hoto ba.

Kamar de yanda kake amfani da hotunan cikin wayar ka kuma kana dorawa akan wallpaper na wayar ka ko nace Fuskar wayar ka.



To shi wannan application zai baka hotuna kala daban-daban wanda zakayi amfani da su ka dora akan wayar ka.

Ga link din application din a kasa sai ka taba ka sauke wannan application din a wayar ka.


Download

Previous Post Next Post