Yanda zaka kalli kowane kalar film a kyuta 2023😍😍

Assalamu alaikum barkan mu da warhaka ya zafi da kuma shirye-shiryen Zaben gwamnoni. To Allah ya shige mana gaba ya kuma bamu shuwagabanni nagari ameen.

Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne wanda zai baka damar kallon dukkanin wasu fina-finai na series ko movies na kasar korea. 

Kowa akwai ra'ayin sa na bangaren kallon fina-finai. Wasu china wasu india wasu america wasu kuma nigerian film wasu kuma namu na hausa.

To duba da yanda muke kul da dukkanin masu bibiyar mu da kuma tambayoyin da kukeyi mana. Hakan yasa na kawo mana wani application da zai baka damar kallon dukkanin nau'i na fina-finan korea. Kowane kala ne.

Akwai dalilai da su ka sa na kawo wannan application din saboda shi wannan application din zai baka damar kallon duk wani series Episode by episode sannan da duk wani film da yayi shura na korea. Sannan akwai bangaren movies wanda zaka gansu guda daya ne ko biyu shikenan sun qare.



Da zarar ka bude application din idan ka shiga bangren movies zakaga ya jero ma duk movies din da kake so ka kalla

Koda ka dade kana neman irin sa to zak ganshi acikin wannan application mai muhimmanchin gaske.


Sannan fannin series zai fito ma da suna bayan nan idan ka shiga zaka ganshi gaba dayan sa kamar yanda kuke ganin a hoton sama.

Bugu da wari shi wannan application din kowane movies ko series idan zaka kalla akwai subtitle na turanchi a cikin sa. Wato ana fassara ma da turanchi kenan.

Akwai adadi mai yawa na dukkanin nau'in film na korea sannan da fassarar turanchi.

Bayan nan wannan application din bashi da wani nauyi sosai saboda gudun ko zai cika ma waya bangaren storage.

Ya kamata kanmallaki wannan application din ko ka ajje shi domin amfanin wani lokchin.

Saboda haka ga link din sa nan a kasa sai ka taba ka dakko application din a wayar ka.

Zakaga na rubuta Download da koren rubutu sai ka taba.

👇👇👇👇👇


 Download

Previous Post Next Post