Yanda zakayi Siyayya Daga kasar waje a kawo ma har Gida Kyuta a wayar ka🥰🥰.

 Assalamu alaikum barkan mu da warhaka. Yan'uwa wani sauki na kawo mana wanda daman tun asali akwai ahi sai de wadansu basu san da shi ba shi yasa na kawo mana baki daya domin muyi amfani da shi.



Application ne da zai baka damar siyayya online daga kasar waje kuma a farashi ( price ) mai sauki sannan koda ace abu qarami ne wato koda memory waya ne ko headphone to zaka iya siya daga kasar waje zuwa inda kake a dan kankanen lokachi zai zo ma.

 Wannan application zan ajje muku link din sa a kasa sai kuje ko dakko shi a wayoyin ku.

Amman zan danyi muku bayani koda kadan ne da kuma hanyoyin da zaka sami sauki wajen amfani da shi insha Allah.

 Da farko idan ka dakko application din zaka bude account normal kamar yanda kake bude kowane application wato ka saka gmail da sunan ka da kuma garin ka da kasar ka.

Bayan ya bude shine zai nuno ma asalin kan application din. Sannan dole sai ka bude account din sannan zakniya siyayya ta ciki. 



Amman koda baka da account normal zakniya ganin komai da yake a cikin application din ko nace Store din da kuma kudeden su.

To bayan ka bude account din sannan application din normal ya bude ma kuma kaga kayayyakin ciki. Sannan koda baka ha abinda kake so ba zak iya rubutu sunan sa. ko menene Sannan koda ma baksan sunan sa ba zaka iya daukr hoton ta sa acikin application din.

To zainkawo ma dukkkanin ire-iren sa sai k zabi kalar sannan ka siya.

Idan ka bude application din zakaga alamar camera tanan zaka dauki hoton abinda idan bakasan sunan shi ba.

 Misalin hoton shine. Watakila kaga wani agogo ko riga ko wani abu a wajen abokin ka yana amfani da shi to bakasan sunan shi ba. To shi wannan application din ta ciki akwai camerar da zaka dauki hoton wannan agogon da yake hannun abokin ka ko rigar ko wayar ko de ma menene shine shi application din zai kawo ma da sunan sa da kuma kudin da zak iya siya.



Bayan ka zabi abinda kake so akwai kalar da zaka zaba da kuma adadin da kake so na wannan abinda kakeson siya. 

Bayan nan zai baka damar idan zaka siya.

Idan ka danna wajen siya to zai baka damar ka cike wani Form.

Wanda yake kunshe da sunan ka da kuma inda kake so ya kawo maka da number wayar ka. Sai kuma han yar da zai baka damar ka saka abin Bankin ka wato ATM.

   Shi kuma wannan ATM din naka akwai number bin da zai dinga fada ma sannan yana nuna ma alamar abinda zak saka a jikin wannan ATM din naka.

Sannan kada ka damu babu wani abu da zasu dinga dauka ko kana tunanin zasu cuce ka. Guaraantee wannan application normal bashi da wata matsala.

Koda irin kayan waya ne misali Speaker ko Screen din waya ko jakar waya normal zaka iya siya ta cikin wannan application din.

             ABIN LURA.

Abin lura anan shine: Amman dukkanin wanda yake zama a Nigeria yanzu kasar ta hana kayi siyayya a kasar waje da kudin Dollar sannan kasa ATM din ka normal na wanda muke amfani da shi a irin bankunan mu.

Dan idan ka takurama zasu iya kulle ma ATM din wannan laifin Nigeria ne. Sai de ka sami mai Account din Dollar ko kaje a bude ma a banki sannan a baka ATM to idan na Dollr ne normal zaiyi amfani kayi siyayya koda ta nawa ce.

Sannan idan baka sami zuwa banki an bude ma ba. Zaka iya samin na abokin ka ko dan uwan ka.

Ko kuma ka sami irin wallet din da suke bayar da Dollar a online irin su Chippercash da sauran su.

Acikin abubuwan da zaka zuwa a wannan form din da zakayi siyayya akwai Portal code (Zip) wanda tashi zasu yi amfani da shi su turo ma har inda kake.

To shi wannan Zip ko Portal code din idan bakasan da shi ba. Kaje google sai ka rubuta Sunan local government ko unguwar ku sai ka rubuta sai ka saka Zip a gaba ko portal code MISALI: ( FAGGE ZIP ) to google zai baka code din da zaka saka a gurin.

Sannan zaka iya bibiyar wannan kayan da ka siya a wannan application kaga inda yake koda ya taho.

To yana zuwa za'a kira ka a number da ka saka ko a tura ma Message a tambayi inda kake sai a kawo ma ko kuma ace kaje ka amsa.

Wannan na danyi bayani ne kadan da kuma abubuwan lura acikin wannan application din.

Saboda haka sai ku sauke application din a wayar ku.

A kasa zaku ga an rubuta Download da koren rubutu sai ku danna shine zai sauka a wayar taka sannan kayi amfani da shi.

👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post