Ta wannan app din zaka iya gane matar ko ka yayan ka 2023

Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a yau a sabon darasin namu wanda na kawo mana wani application da zai bamu damar control din wayoyin mu dana matan mu dana yayan mu.

Wato shi wannan application din amfanin sa ya wuce inda yaje saboda zai baka damar kulle asalin wayar ka batare da ka kashe ta ba. Hasalima idan ka saka lokachin da wayar zatayi sleeping wato ( Bacchi) zaka iya danna gurin lock screen zata dan farfado amman de baza ka iya amfani da ita ba sai wannan adadin lokachin da ka saka mata yayi sannan zaka iya amfani da ita duk nisan kwanaki ko ranaku ko awowi hatta mintuna ma.



Haka bangaren wani abu da yake acikin wayar wato kamar application kenan. Zaka iya saita wani application da zai daina aiki acikin wayar zuwa wani adadi wanda babu ta yanda zaka iya amfani da wannan application din inde lokachin da zaiyi aiki a wayar taka bayyi ba.

Nasan wani zaiga kamar ta tsuniya nake karantawa. To ka tabbata da cewa kayi mistake din kulle wayar ka babu tabyanda zaka bude ta inda kabayi la'akari da mintuna ko sakannin da kake so ka gwada app din a wayar ka ba. idan zata wuni sai wannan lokachin yayi sannan zaka iya amfani da wayar ka. Saboda asali idan kasa application din a wayar ka zayyi amfani da Admin App kuma mafi yawanchi munsan yanda admin app yake control din waya. Sannan idan ka saka ta a wannan sleeping din babu ta yanda zaka kashe wayar ballantana ka bude screen din ta. Kai koda ma kayi kokarin kashe wayar to da zarar ka qara kunna ta zata tafi wannan sleeping din har sai adadin da ka saita a wannan app din yayi sannan zatayi amfani.

 AMFANIN APPLICATION DIN.



Amfanin wannan application shine zaka iya sakawa yayan ka ko matanka  ko kuma kaima da kanka. Misali kamar dalibai kana so kayi karatu ko wani aiki to wayar taka ta hanaka wannan abinda kake so kayi. Zaka iya saitawa bama zatayi aiki a lokachin ba saboda amfani da wannan application din.

Idan yayan kane ko matan ka suma zaka iya saitawa duk lokachin da baka so suyi amfani da wayar tasu. Sannan koda ma sun gamo inda application din yake basu da hanyar iya cire shi saboda yana amfani da admin app zaiyi wahala su gani hakan.

Sannan kuma zaka iya amfani da hanyar boye application din a wayar fash bama zasu gane inda app din yake ba.

Kawai sai de su dinga ganin wayar tana kullewa da zarar lokachin da ka saita musu yayi.



Idan ma ba duka wayar zaka dinga kullewa ba zaka iya zabar wani chatting acikin wayar ka kulle shi.

Kuma bugu da qari zaka iya saitawa dau daya amman ka saka dukkanin lokachin da baka so ayi amfani da wayar.

Ina mai tabbatar muku da wannan application mai tsadar gaske yana da amfani sosai.

Ta cikin app din zaka iya ganin adadin lokachin da akeyin amfani da wani application da kuma minti nawa ko awa nawa rabon da a bude wannan application din.




Akwai abinda ya danganchi Guri ( Location ) Shima zaka iya saitawa inde anje wannan gurin to wayar bazatayi amfani ba ko wannan application din da ka saita bazaiyi amfani a wayar ba. Kamar irin makaranta haka ko wani guri mai mahimmanchin gaske.


 GARGADI!.

Ya zama wajibi wajen saka lokachin ka tabbata ka saka iya adadin da kake so dan idan kayi mistake ka saka wanda ya wuce tunani to wayar nan a wannan ranar ko wannan yinin ko satin bazata taba amfani ba.

Saboda na gwada kuma na sannan illar wannan.

Ga dai link din application din a kasa sai kaje ka taba zaku ga na rubuta Download sai ka taba ka sauke shi acikin wayar ka. 

Sai ka saka acikin wayar da kake so kayi amfani da shi. 


 Download

Previous Post Next Post