Yanda zaka ajje lambobin wayar ka akan Memero ( Sirri ) 2023

 


Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi.

Ina fatan kuna cikin koshi  lafiya Allah yasa hakan ameen.

Yan'uwana yau wani application ne na kawo mana wanda zai taimaka mana bangaren contact wato numbobin wayar mu da muke save a kan waya ko gmail ko kuma akan SIM na layin wayar mu.

To duk ire-iren wadannan abubuwan da akw ajje numbobin sukan iya samun matsala ka rasa wadannan numbobin amman da taimakon wannan app din zaka iya ajje dukkanin lambobin akan memory ko flash ko gmail din ka.

Saboda zai mayar ma da su waje daya yayi save dinsu sannan Zero KB zakaga ko KB 1 bai kai ba.

Dukkanin nauyin ko yawan lambobin bazasu cika ma wayar taka ba.

Bayan nan koda ka chanja waya inde wannan file din yana nan zaka iya dawo da dukkanin lambobin akan sabuwar wayar taka. Da zarar ka dakko shi app din a wayar taka zai ma Restore din contact din gaba daya.

Amman de zan ajje muku videon cikakken bayanin application din.

Ga shi nan a kasa sai ka taba ka kalla.

👇👇👇👇👇👇

Kamar yanda kuka gani acikin wannan videon duk nauyin ko yawan lambobin zaka iya ajje su waje daya har sai lokachin da ka buqa ce su.

Sannan ga link din application din a kasa sai ka taba kayi download din sa a wayar ka.

Amman na manta tun farko ban fada muku akan app din na wayar iphone bane.

Ga link din App din

👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post