Application guda biyu da zaka gano wayar ka ta Hanyar Tafi koda ta bata 2023

 


Application guda biyu na tura komai kyuta (Free) Da Hanyar da zaka gane wayar ka ta Amfani da Tafi (Clap) koda ta bata.

Assalamu alaikum barkan mu da safiyar yau. Yan'uwa wani application ne da zai baka dauki wajen tura duk abinda kake so zuwa inda kake buqata dan'uwan ka ko abokin ka ko wata ma'aikata ko makaranta. 

Zan fara bayani akan application na farko sannan a kasa zanyi na biyu.

(1) Shi wannan hanyar zakayi amfani da ita ka tura video ko file ko decument duk nauyin sa sannan batare da ya rage kwaleti ba ( Quality). 

 Wannan hanya ta itane manyan gidajen talabijin suke amfani da ita wajen tura dukkanin sakonnin videon wani shiri inda ake haskawa.

Nasan da yawa mutane suna ganin kamar duk shirin videon da akayi sai an kawo shi gidan tv inda za'a haska sannan. To amman wani lokachin zaka iya ganin inda mutumin da yake wannan shirin gaba daya ba a kasa daya bane ma ballantana yazo har garin sannan a haska shirin nashi ko a haska film din.

To ta irin amfani da wadannan hanyoyi ne ake bi ake tura video duk nauyin sa zuwa inda kake so batare da ya rage haske ko mb ba.

 Idan kabi hanyar turawa ta whatsapp ko telegram ko wata hanya zakaga wannan abinda ka tura ya rage kyu da mb sannan zakaga sun baka ka'idar adadin da suke so ka tura video idan ya wuce haka bazai turu ba. 

 Bayan nan idan kabi hanyar  to dukkanin ku ne zakuyi asarar Data domin wajen turawa za'a ja maka Data sannan shima wajen download za'a ja masa Data mai nauyin gaske.

Amman idan ka bi wannan hanyar wajen dorawa gaba daya bashi da wahala ballantana ya ja maka MB na Datar ka. Kawai zai baka hanya biyu wadda zaka iya turawa a dakko videon.

(2) Application na Biyu shine zaka gane wayar ka koda ta Bata ta amfani da Tafi.

Da zarar ka nemo wayar ka ka rasa kana tafi da hannayen ka kawai wayar taka zatayi qara tare da kunna fitilar wayar ka ( Glash) .

Saita shi babu wahala kamar de yanda kuka gani acikin videon da nayi bayani.

Ga link din sa nan a kasa tare da app na farko.

Ta hanyar turawa  ta gmail ko ta copy link wanda zaka turawa mutanen da zasuyi amfani da videon duk nauyin sa.

Kawai abinda ake da buqata ka create din account acikin app din sannan.

Zakuga na rubuta App na farko da kuma App na biyu shine link din kawai sai ka taba shi.

App na Farko

👇👇👇👇

Download

App na biyu

👇👇👇

Download


Previous Post Next Post