SIRRI//Yanda zaka bude kowane security ta agogin wayar ka// 2023

Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi ina fatan na same ku lafiya.

Yan'uwa a gurguje yau darasin mu akan wani application me da zai baka damar kulle dukkanin abubuwan d ake cikin wayar ka wanda babu wanda zai iya bude ma shi.

Akwai application da yawan da suke ba da dama kana kulle duk wani sirrin da yake chat din ka ko hotuna ko videos din wayar ka.

To amman Zakaga wani lokachin ana samun wani a gida ko abokin ka yana gane duk password din da kake amfani da shi wajen kulle bayanan sirrin ka.

Idan ma ba haka ba akwai hanyoyin da zai iya bude wannan password din naka.

To shi wannan application da na kawo mana yana da matuqar tsaeo saboda zakayi amfani da duk wata kafa da zaka bayar da kafa wajen bude pasword din wayar taka.

Zaka amfani da agogin wayar ka wajen budewa. Koda misali ka bude password din a ganan mutum to koda ka bashi bazai iya budewa ba saboda duk mintuna agogon gana chanjawa.

Kuma ya danganta da yanda ka saita agogon zaka iya saitawa awoyi da kuma mintuna ko mintuna da awoyi. Ko kwanan wata da mintuna da dai duk yanda ka ga damar saitawa. Saboda acikin application din za'a baka zabi wajen saita password din.

Ga dan misalan zabin nan a kasa cikin hoto.


Kamar yanda kuke ganin zabukan suna da yawa sosai wajen saitawa babu wanda idan ka saita zai gano hanyar da zai bude wannan application din da ka saka wa security.

Amman zan danyi karin bayani akai duk de da na saka muku cikakken bayanin a kasa zakuga na ajje wani video to idan ka bude shi zakaga yanda zake saita application din da ma yanda ake dakko shi.



Idan ka zabi mintuna da awoyi to idan zaka bude wayar taka zakayi la'akari da karfe nawa da mintu nawa acikin wayar ka a lokachin da kake kokarin budewa wannan sirrin naka. To idan ka saka shine zai bude idan kayi mistake akan wannan lokachij to bazai bude ba.

Idan kuma ka saita da kwanan wata to shima zakayi la'akari da nawa ga wata da kuma awa ko mintunan wayar taka a lokachin sannan zai bude.

Duk mintuna password din yana chanjawa to kaga koda ka bude a gaban wani bazai gane da mintuna yake budewa ba idan yasa daidai mintun da ka bude a gaban sa to bazai bude ba saboda a lokachin mintunan sun chanja.

Kuma wajen saka password din daman guda hudu ne misali 07:01 a password din da zaka saka shine ( 0701) haka idan 10:30 ne shi kuma ( 1030 ) ta hakane zaka dinga bude password din.

Ga cikakken videom darasin a kasa ka taba sai ka kalli yanda ake amfani da shi.




Ina fatan ka kalli wannan videon sannan ka gane yanda ake amfani da app din.

Sanan shi kuma link din application din gashi nan a kasa zakaga an rubuta Download sai ka taba shine zaka sauke app din acikin wayar ka. 

👇👇👇👇👇👇👇

 Download

Previous Post Next Post