Tabbas Ana Bibiyar Sirrin wayar ka Baka sani ba/ Amman ga mafita 2023

TABBAS ANA BIBIYAR SIRRIN WAYAR KA BAKA SANI BA.

Assalamu alaikum barkan mu da safiya. Ya zafi kuma Allah yasa mu wuce Lafiya Ameen.

Yan'uwana yau wani application na kawo mana da zai baka damar gano duk wata kafa da ake bibiyar sirrin ka sannan kuma koda wayar ka tana baka matsala wannan hanyar duk zaka magance wannan matsalar.

Abu muhimman da ya kamata mu sani akan wannan darasi shine. Na Farko shin ko kasan za'a iya bibiyar al'amuran ka baka sani ba. To Tabbas ana iyayin hakan. Za'a saka ma Applicatioj na daukar duk kirin da kake ko na daukar duk location da kake ziyarta ko camera baka sani ba.

Saboda ire-iren wadannan application din idan aka saka maka za'a iya boye ma bazaka taba ganewa ba.

Bugu da qari wani lokachin zaka iya siyan wata wayar amman akwai wata game ko application da zai iya buya acikin wayar taka domin a haka wayar tazo.

Sannan abu na biyu akwai application da yake amfani a background wanda yake shanye maka chaji ko yake shanye maka Datar da ka saka acikin layin wayar ka.

Akwai matsalolinda yawan da baka san da su ba wanda shi wannan application din zai binciko maka.

Idan ka mallaki wannan application din zai binciko ma duk wata kafa da kake zargin ana bibiyar ka ko an saka ma wani app wanda zai cutar da kai ko wayar ka.

Sannan wani lokachin zaka iya saka wani application din sannan ka bashi permission a wayar ka to sai daga baya zai dinga bawa wayar ka matsala. Amman kai baka sani ba To shi wannan application din zai ware ma dukkanin wani app da yake bawa wayar taka matsala ya baka damar cire su.


Sannan ga video nan a kasa idan ka kunna videon ka kalla normal zaka ga yanda ake saita application din a wayar da duk yanda zakayi amfani da shi.

Sannan achan kasa zan ajje muku link din Application din domin kuyi amfani da shi.

Ga videon nan a kasa.

👇👇👇👇👇


Kamar yanda kuka gani acikin videon sama da na ajje muku zakuga hanyoyin da yawa da bakasan da su ba. Sannan koda ma kaga wani app da aka boye ma to zaka iya cire shi ta cikin wannan application.


Ga link din Application din a  kasa sai kuje ku dakko shi.

Zakuga an rubuta Download

👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post