Wayar ka sirrin ka🥲// Ga wani App na boye sirri waya ( HICONT )

 Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a saboj darasin namu.

Yau darasin mu zai koma akan abinda yake damun mutane da yawa ne. Wato number waya. Da yawa kana so kayi save din wata number amman kana tunanin za'a iya daukar wayar ka sannan aga number hakan yake sakawa mutane da yawa basa saka full sunan mai number acikin wayoyin su. Misali idan sunan mace ne sai mu rubuta wanai suna daban na aboki ko na wani customer a kasuwa kawai saboda gudun idan kaje gida matar ka ko abokin ka zai iya gane number waye.





Ko kuma wani lokachin sabida kana tunanin za'a gane number kanwar ka ko er gidan ku saboda aboki ya takurama sai ka bashi number kuma tabbas wata rana inde wayar ka taje hannun sa zai iya daukar wannan number.

To shi amfanin wannan application din zaka boye dukkanin wadansu numbobi da bakaso asan dasu acikin wayar ka. Sannan batare da kayi block din ko daya daga cikin ba.

Idan ka shiga cikin application din zaka zabi adadin numbers da kake so ka boye da zarar ka boye to koda za'a rubuta full sunan mai wannan number ko full number to baza ta nuna asali akwai  number a wayar ka ba.

Wato kamar yanda hausawa sukace. "Mai hankali ne kadai zai gane dingishin kwado"😄. Nima na tana hausa yau. 

Ina nufin sai wanda abin ya faru dashi zai gane amfanin wannan application din. Amman tabbas kuna buqatar sa domin wata rana amfaninsa zai zo muku.





Kai da wayar ka baka da damar ajje number da sunan da kaga dama saboda gudun kada a gane mai number a wajen matar kane ko wajen abokai.

Ga videon cikakken bayanin wannan application din a kasa zaku ganshi kawai ka danna sai ka kalli yanda ake saita shi da yanda ake amfani dashi a waya.

👇👇👇👇👇👇👇



Ga link din Application din a kasa sai kaje ka mallake shi a wayar ka. Amman ina fatan ka kalli videon domin ka saita shi yanda ya kamata.

Ga link din a kasa zakaga na rubuta Download da koren rubutu sai ka taba shine zai baka damar mallakar shi a wayar ka.

👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post