Yanda ake hada cartoon a kowace kalar waya Android ko Iphone 2023

 Assalamu alaikum barkan mu da safiya ina fatan kun tashi lafiya kamar yanda na tashi Alhamdulillah.

Yan'uwa wani video ko nace darasi na kawo mana mai matuqar amfanin gaske da zakayi mamaki idan ka mallakeshi kuma ka fara hada cartoon da kanka. Application ne na hada cartoon kamar de yanda kake ganin mutane suna hadawa tare da abin darriya ko wani darasi ko dirama. To nasan wasu suna da buqatar suga suma suna hada ire-iren abubuwan nan amman mutum sai yace bashi da computer da zai hada.

A takaice de na kawo muku application da zai baku damar hada carton kowane kala acikin wayoyin ku batare da kun mallaki computer ba. Sannan kowace kalar waya ce zakayi amfani da wannan app din.



Ina nufin Android ko iphone baki daya.

Acikin wannan rubutun zan ajje muku cikakken videon yanda ake hadawa da kuma link din application din na dukkanin wayoyin guda biyu.

Amman zan danyi muku karin bayani akan application din.

Da farko idan ka dakko application din sannan ka bude shi kamar yanda kake bude sabon application normal zaka jira har ya gama budewa. Sabo da hakikanin gaskiya application din saboda abubuwan da yazo dashi yana da dan nauyi kafin ya bude. Amman idan babbar waya gareka baka da wata matsala aciki.

Sannan duk dan wani nauyi da ya nuno ma sai ka dan jira har sai ya gama sannan.

Kana budewa zai nuno ma fresh yanda app din yake sannan zakaga creat sai ka taba. Acikin mutanen da ka zaba wanda zakayi wasan da su da kuma dora murya duk abinda kaga akwai alamar hoton hular sarki to wannan sai ka biya sannan zakayi amfani da abin. Wato ina nufin Premium app kenan. App a na kyutar ma zaka iya hada abin mamaki sosai. Idan kuma har kasan zaka mayar da hankali akan app din to ko nawa zaka iya biya domin amfani da komai-da komai na app din.

Application din zaka zabi mutanen da kake so ka hada duk abinda kake so. Da kuma guri da kuma yanayin da kake so su kasance. a zaune ko a tsaye ko suna tafiya. Sannan zaka dora musu muryar da kake so. A lokachin hada cartoon din akwai gurin recording zaka danne sai kayi magana za'aga kamar cartoon din ne yayi magana aciki.







Kawai ga link din videon carton din nan guda biyu zan ajje muku idan wannan bai gamsar da kai ba nasan wani zai gamsar da kai.

To kowane sai ka taba ka kalli idan kuma wanda ka taba ka gane komai to Masha Allah haka ake so.

Idan baka gane ba sai ka tana na biyu dukkanin su nayi sune domin ku gane yanda app din yake.


VIDEO NA FARKO

👇👇👇👇👇👇



VIDEO NA BIYU

👇👇👇👇👇👇



Dukkanin videon da na dora muku suna da amfani sosai. Kuma a cikakken bayani nayi muku har yanda ake dora murya.



Ga kuma link din application din a kasa na dukkanin wayoyin guda biyu na iphone din da kuma android din.

Idan wayar Android gareka zakaga ANDROID APP da koren rubutu to sai ka taba shine zaka sauke shi acikin wayar ka.

Idan kuma iphone ne zakaga an rubuta Iphone App shima kana tabawa shine App din zai sauka a wayar ka.

👇👇👇👇👇


Android App

Iphonr App

Previous Post Next Post