Yanda zaka hana ayi Tracking din wayar ka Aga inda kake da zamašŸ„² 2023

 


Assalamu alaikum barkan mu da warhaka.

Yau darasin mu wani application ne da zakayi amfani da shi wajen biye asalin inda kake wato location dinka kenan.

Shin ko kunsan akwai applications da kuma websites da yawan gaske wanda suke bibiyar mu a koda yaushe suna ganin sirrikan inda muke zama. Sannan kowane lokachi za'a iya nemar ka wato ayi tracking din ka saboda a gano a inda kake. Duk baka sani ba.

To shi amfanin wannan application din zai baka damar ka boye asalin inda kake da zama sannan ka zabi inda kake so koda anyi kokarin gano inda kake baza'a gani ba gaba daya.

Wato vartual loaction kenan.

Sannan koda idan kana so ka ziyarchi wani website sin ko ka bude wani application zaka iya kunna wannan apps din wanda na kawo muku. Idan ka kunna shi zai baka damar chanja asalin inda kake babu wanda zai gano a ina kake ballantana ya bibiye ka.

Nayi bayanin wannan application a cikin video yanzu hak yana kan youtube dina zaku iya search din kk Techtube a youtube bayan kun bude zaku ga acikin videos din akwai wannan wanda zaku kalla tun daga yanda ake dakko app din har yanda ake amfani da shi.

Kafin na danyi muku qarin bayani akan application din ina snaar daku kuje chankasa zakuga link din app din sai ku sauke  shi a wayar ku.

Da farko bayan ka dakko application din to normal zaka bude shi kamar yanda k saba bude sabon application. Bayan ka bude shi ya nuno ma map acikin app din to sai ka fita ka nome setting din kan wayar ka.

Bayan ka nemo sai ka nemo about phone acikin nan zakaga Build number sai ka taba shi sau 7 Da sauri shine zai nune ma sainka saka password din wayar ka wadda kake bude wayar taka.

Bayan nan shine developer potions zai bude sai ka nemo shi acikin setting din idan baka ganshi ba sainkayi search din shi.

Bayan nan sai ka je kasa acikin rubutun da ya nuno ma zaka ga select mock location idan ka taba to zakaga wannan app dinw anda ka dakko to sai ka taba shi.

Idan ka taba sai ka koma cikin application din.

Daman tun farko mun bude shi. Sannan zakaga map ya nuno ma to abinda zakayi acikin map din nan na  app din zaka zabi dukninda kake so unguwa ko gari sai ka taba kana tabawa a sama zakaga Apply sai ka taba apply din.

Idan ka taba shikenan zai nuno ma yayi.

Shikenan ka chanja location din ka babu wanda zaiyi tracking din ka

Ga link din application din a kasa sai kuje ku dakko app din.

Zakuga na rubuta Download da koren rubutu idan kuka taba shine zaku sauke shi a wayar ku.

šŸ‘‡šŸ‘‡šŸ‘‡šŸ‘‡šŸ‘‡šŸ‘‡

Download

Previous Post Next Post