Yanda zaka kma barawon wayar ka koda ya kashe wayar

 


Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a yau a sabon videon namu. Yau wani application me da zai baka damar gano wayar ka a duk inda take koda an kashe wayar.

Ina nufin. Wannan application din da zarar ka saka shi acikin wayar ka kuma ka saita shi kamar yanda na nuna muku acikin videon da na dora a youtube to idan wayar taka ta bata ko ka neme ta ka rasa ko aka sace. Zaka gano duk inda take. Da yawa idan aka sace waya akan kashe ta ne idan kuma irin su Samsung ne zakaga sai an saka Password din wayar sannan wayar zata ba da damar a kashe ta. To barayi sukan bi wata hanya ta amfani Airplane mode. Wanda zasu kashe duk hanyar da za'a iya track ko a kira saboda gaba daya network din wayar suke kashewa.



To da taimako wannan application din zaka ita gano wayar ka koda an kashe ta. Saboda idan aka kashe waya koda police station kaje baza'a iya track din ta ba sai am kunna ta sannan. Amman shi wannan app din zai taimaka sosai. Domin asali zai ba da damar ayi Fake Shutdown wato wayar zata mutu ko a danna wajen kashewa amman wayar gaba daya ba mutuwa tayi ba.

Amman wanda ya dauke ta zaiga alamar ta mutu saboda duk wani abu da zaiyi wayar bazata kawo ba.

To ta hakane zaiga kamar ya kashe wayar amman a kunne take. Ta hanyar ne za'a iya track din wayar. Sannan koda sunyi amfani da Airplane mode. Shima app din zai taimaka ya bada Fake airplane mode. Wannan shima na karya ne.

Sannan akwai  fannin Intrueder wanda zai ba da damar daukar hoton duk wanda yayi kokarin saka security na wayar sau adadin da ka saka ko ka saita.


Ga shi nan dai link din Application din a kasa zakuga na rubuta Download da babban rubutu da kuma koren rubutu idan ka taba shine zai baka damar saukewa a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇

DOWNLOAD

Previous Post Next Post