Yanda zakayi amfani da duk application na kudi ake cire talla kyuta ( Free )

 Assalamu alaikum warahmatullah barkan mu da sake kasancewa a yau a sabon darasin namu.

Yau wani application na kawo mana wanda an dade ana jiran wannan app din domin muhimmanchin sa .

Amfani application din shine zai baka damar kulle duk wani application da yake da talla a wayar ka kowace kalar wayar taka iphone ko Amdroid.

Akwai app da yawa da muke buqatar amfani da su a wayoyin mu amman zamu ga saboda tallolin da suke aciki yake sawa muna tsanat app din.

Saboda wani application din zakaga tallan ta wuce tunani kuma zasu ce idan kana so ka cire wannan tallan sai de ka biya kudi ka sayi premium shine babu talla aciki.

To da taimakon wannan application da na kawo mana shine zai baka damar kulle duk tallolin da suke a kowane kalar application. Sannan shi app din da farko idan kana so ka kulle tallolin zaka shiga cikin application din bayan ka shiga zakaga wajen kunnawa a tsakiyar application din. To idan zaka kunna shine zaka danna to da zarar ka danna zaka iya shiga kowane application sannan bazakaga tallan da take a cikin sa ba koda tallan tana da yawa. Sannan a lokachin idan ka shiga cikin application din na dace talla zakaga adadin yawan tallolin da ya kulle ma.

Sannan idan kana so ka kashe application din normal komawa zakayi cikin app din sai ka kashe gurin inda ka kunna din nan a farko.

Sannan shi application din babu wata wahala wajen amfani da shi sannan koda nauyin app din bashi da yawa ko nace MB din app din.

Ya kamata ku mallaki wannan application.

Ga videon cikakken bayanin wannan application din.

Sannan acikin videon ma zaka koyi yanda ake saita application din da yanda zaka kulle tallolin.

Kawai ka taba kan hoton videon zai bude.


Kamar yanda kuka gani acikin videon yanda ake saita app din.

Sannan ga link din application din a kasa na dukkanin wayoyin guda biyu.

Android da kuma iphone din.

Idan wayar android gareka zakaga an rubuta Android app idan kuma iphone ne zakaga iphone App.

Da zarar ka taba shi shine zaka sauke app din a wayar ka.

Android App

Iphone App

Previous Post Next Post