Yanda zakayi control din wayar ka bayare da ka taba ta ba ( Sirri ) 2023

 


Assalamu alaikmu ina muku barka da wannan lokachin. Sannan ina mai taya mu murnar samun garabasar kwanaki goma na farkon wannan watan na babbar sallah. Allah ya karbi ibadun mu ameen.

 Yan'uwa yau wani application na kawo mana wanda zai baka damar control din wayar ka batare da ka taba wani bangare na hardware wayar ba. 



Nasan wasu zasu tambaye menene (Hardware) Hardware shine dukkanin abun da muke gani kuma muke iya tabawa a jikin waya ko a computer baki daya. Misali: ( Volume,Battery,powerbutton,da screen, da kuma wayar baki dayan ta.). Duk wani abu da kake ganin shi ajikin wayar ka kuma kana iya tabawa shine hardware. Amman banda keyboard na waya tunda shi zaka ganshi idan kana chatting amman kuma bashi kake tabawa ba screen kake tabawa saboda shi iya gani akeyi amman ba'a iya tabawa sai de anyi design din sa idan ka ganshi zaka iya amfani da screen na wayar ka sannan kayi amfani dashi wajen rubutu.

Amman kaga koda gidan wayar ka da kake sakawa shima zamu kirashi da hardware. Sannan harda su Speaker tunda kaga speaker ana iya cire ta ka taba. Wannan duk qarin bayani ne domin ku fahimchi karatun.




 To zaka iya amfani da wayar ka batare da ka taba wani hardware a jikin ta ba.

Misali idan kanaso ka karo volume na wayar to kaga dole sai ka taba volume a jikin wayar kaga shima hardaware ne ko kuma inda ake kashe wayar sannan a kunna dukkanin su hardware ne. To zaka iya amfani da wannan application din a matsayin kayi control din irin su.

 Ko kuma a jikin screen din wayar taka wani guri baya dannuwa kamar shiga wajen kallo ko wajen hotuna ko wani bangare na wayar. Dukkanin wani bangare zaka iya chanja shi wajen amfani da wannan application domin gano dukkan abinda kake so.

 Alla yasa kun gane me nake nufi saboda burins shine ku gane sannan kuyi amfani da shi.

 Akwai application a kowace kalar waya android ko iphone dukka.

Amman amfi yawan chi a iphone akwai insa zaka iya kunnawa batare da ka dakko wani sabon application ba.

 Ita kuma wayar android akwai application da yawan gaske wajen amfani da ire-iren su.

Shi yasa ma na kawo link din application na wayar android din sai kuyi amfani da shi.

 Ga shi nan a kasa na rubutu download sai ku taba ku sauke shi a wayar ku.

👇👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post