Yanda zaka dawo da Duk Lambobin wayan da ka Taba gogewa na Adadin Lokachi 2023

Yanda zaka dawo da Duk Lambobin wayan da ka Taba gogewa na Adadin Lokachi 2023


Assalamu alaikum warahmatullah wa barakatuh. Barkan mu da safiyar ranar alhamis. Yan'uwa wani application ne na kawo mana wanda zai baka damar dawo da dukkanjn numbobin da ka taba rasawa a wayar ka. Akwai applications da yawa da kuma hanyoyi da yawa yanda zaka iya dawowa da duk wasu numbobin da ka taba rasawa. Sai de dukkanin su zaka duba kaga wace hanya ce tafi dacewa domin koyawa yan'uwa.



 Mutane sukanyi korafi a wajen comment na ire-iren application din da nake kawo wa akan basayi ko kuma suna da wahala wajen saitawa ko suna magana akan na dingayin irin na wani ko wasu wanda suke koya Tech a social media.

 Maganar application dukkanin wanda kuka ga suna koyar da Tech ko suna kokarin koya babu wanda zai kawo ire-iren App din da nake kawowa saboda mafi yawan chin wanda nake bayar wa zaku ga basu fiye shiga mutane ba wato masu tsada ne. Shi yasa idan kana da dan karamin sanin ka ba lalle ka gane lokachi daya yanda ake amfani da application din ba.

Maganar bayani sosai yanda ake saita app din mafi yawanchin ku sunsan ina da youtube kuma duk ina bayani full a youtube har yanda ake amfani da shi. Amman maganar bayani a facebook kowa da yanda ya sabawa page din sa yanda yake gabatar da abu. Bayan nan in har muka saba muku da sai mun nuna yanda ake amfani da app din to wallahi da yawa zasu yi kasala bazasu dinga bincike ba wanda mu so muke muga kowa ya iya da kansa.

Bana kwaikwayo kowa abinda na iya shi nake yi Afwan.



Idan kana so ka dawo da lambar wayar da ka taba rasawa kamar yanda na fada a farkon rubutun hanyoyi ne da yawa amman na kawo muku wanda zaku iya amfani da shi wajen dawo da su. Sannan idan kayi deleted na number waya sai yayi kwana 30 sannan number zata bar Achive. Achive gurine ko folder ce da take ajje dukkanin abinda aka goge amman ana tunanin za'a iya dawowa da shi wani lokachi. Shi yasa idan kayi deleted na number dai yaje chan ya zauna na tsawon kwanaki 30 sannan zai bar wayar taka baki daya.

Na farko wannan application sama da mutune Billion daya ne suka sauke shi a wayar su.

Da farko dukkanin numbobin da ka dira a wayar ka akwai hanyar da zakayi backup din su automatic to koda ka chanja waya idan ka dora wannan application sai ka yi restore din su ta amfani da gmail din ka.



Ga link din sa nan a kasa sai ka sauke shi kayi amfani da shi.

Nasan ma da yawa kuna amfani da shi amman baku sannan aikin sa ba.

👇👇👇👇👇👇

Download

Na biyu shi kawai amfanin wannan application din shine zai maka backup a google drive ko dropbox idan ka tashi restore din sa direct zai dawo kan wayar ka sanann zaka iya transfer zuwa sabuwar wayar ka.

Na kawo muku wannan ne domin idan kuna so kuyi amfani da su duka biyun shi yasa ma a sama bance app din guda biyu bane.

Amman zan baku shawara kuyi amfani da wancan na farkon. 

Ga link din na biyun

👇👇👇👇👇👇

Previous Post Next Post