Yanda zaka dawo da komai idan ka Rasa ( Messges,contact,callog,apps) 2023

 



Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi yan'uwa ma'abota wannan shafi mai albarka na KK Techtube.

Yau darasin mu kan wani application ne da ya hada abubuwa sama da biyar (5) masu matuqar amfanin gaske.

Zai baka damar dawo da dukkanin abubuwan da ka goge kamar. Lambobin waya. Messages din ka,call log da Apps tare da hotuna.

Amfanin wannan application din shine. Zaka iya ajje dukkanin wadannan abubuwan da na lissafo a sama. Acikin wayar ka ko ka ajje akan memorin ka ko flash ko kuma akan cloud kamar irin su drive ko dropbox da sauran su.

Idan kayi backup din su acikin wayar ka a matsayin folder ko cloud irin su drive din to koda ka chanja waya zaka iya restore din wannan lambobin ko messages din zuwa sabuwar wayat ka.



Duk de da na dora videon a youtube kamar yanda kuka ga full din bayanin akan app din.

Hakan yasa kawai na dan tattauna bayanin kadan anan saboda may be ba kowa bane zaiga videon ba.



Amman idan kana son ganin videon kaje youtube mai suna KK Techtube zakaga full din bayanin yanda ake saita shi gaba daya.

Ga link din application din a kasa

👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post