Yanda zaka dawo da sakonnin ( Messages ) da ka taba gogewa na tsawon lokachi 😍 2023

 Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a sabon darasin namu wanda zamu tattauna akan abinda ya shafi message SMS da kuma Kiran waya Call logs. Wannan hanya zata baka damar da dawo da duk wani sako da kayi a wayar ka kuma aka sami akasi ka goge wannan sakon ko kuma ka neme ahi ka rasa. Da kuma duk wata kiran waya da akayi ma ko kayi.

Na tabbata kuna ta jiran wannan hanyar domin da dama mukan tsinchi kanmu akan rashin ganin wani muhimman message bayan a farko min ganshi amman daga baya mune me shi mu rasa abinda ya shafi text messages din  banking ka ko na wani mutumin ko na budurwar ka. 

Amman lokachi daya zaka neme shi kwata-kwata karasa. To shi amfanin wannan application din shine zai baka damar dawo da duk wani sako messages koda an goge shi ko ka neme shi ka rasa da kuma duk wani kiran waya da ka nema ka rasa.

Shi kiran waya zaka iya tsintar kanka an kira ka da wata number to daga baya ka goge wannan kiran gaba daya to zaka iya dawo da duk wani kiran da kayi ko akayi ma koda kuwa ya dade da gogewa ne.

                      AFWAN.



Farko dole sai ka saka app din sannan kayi backup din sakonnin da kuma kiran waya zuwa daya daga cikin drive sannan zaka iya dawowa da su koda ka neme su ka rasa.

Idan ka shiga app din zai nunama adadin messages da kiran wayar ka sannan zakaga Backup da kuma Restore.

Idan ka danna backup shine zai ajjema wadannan abubuwan koda daga baya kana buqatar dawo dasu to idan ka shiga sai ka taba Restore. Shine zasu dawo cikin wayar ka.

Sannan wajen ajjiyewar zaka iya saita lokutan da kake so shi application din batare da ka ta danna backup ba yana ajje ma su.

Akwai Daily shine kullum da kuma weekly da dai sauran su. Idan ka saita to shi app din duk bayan wannan lokutan zai dinga backup din duk sakonnin ka da call logs din naka.


Bayan nan akwai schedule wanda zaka iya saita wani adadi na lokachi wajen ajje ma sakon da kiran wayar.


A takaice de idan ka mallaki wannan application da kuma amfani da shi kafin ka rasa daya daga cikin sakonnin ka da kiran ka.

Domin zai na baka damar koda ka nemi daya daga ciki ka dawo dashi.

Ga link din application din a kasa zakuga an rubuta download sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.

👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post