Yanda zaka dora wakar ka ko karatu a Audiomack/ Cikin Sauki i dinga saurara 2023



Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a wani sabon videon.

Yan'uwa yau darasin mu akan abinda kuka dade kuna kirane. Domin hanya ce da zaku iya dora dukkanin wakokin kunko wa'azin malamai ko wani karatu a audiomack. 

Da yawa munsan audiomack domin aciki muke sauraron wakoki. Sai de wani yanason yaga ya bada gudunmawa wajen dorawa karatuttukan malamai wani kuma wakokin sa yake so yaga ya fara dorawa domin saurara ga al'umma.

To cikin ikon Allah yau darasin ya kawo mana yanda zaka iya amfani da wata hanya ka dinga dora wakoki ko karatun sannan kowa zai iya saurara sannan zaka iya samun kudi aciki.



Da farko de dole sai kana da account a asalin application na audiomack din sannan sai kayi amfani da application din da na kawo mana yanzu.

Nasan muna da audiomack din a wayoyin mu to amman duk da haka zan ajje muku link din su gaba daya audiomack din da shi dayan application din sannan na kowace kalar waya Android da kuma iphone din gaba daya.

Sai de zaku ga link din sunyi yawa domin kowace waya za'ayi amfani da application biyu ne. Amman de insha Allah zanyi kokari na ajje muku na kowane app domin saukaka muku wajen gane kowane link.

Bayan ka bude account a audiomack sai ka saka irin username da password acikin wannan application din iri daya da wanda ka bude a audio mack.

To shi wancan application din shi zai baka sauki wajen saka wakokin ko karatuttukan ko wa'azin ta ciki. Sannan zaka na ganin adadin wadanda suka saurari audio din ko sukayi comment a aciki.



Amman asali ta audiomack din ake dorawa ta amfani da button ko nace madannin Mylibrary a kasa kanen cikin audiomack.

Bayan k danna shine wannan application din zai bude ya baka damar saka waka Wato Song ko Album idan kana da su da yawa. Bayan ka danna song din idan guda daya ne shina zai baka damar dakko audio din daga kan wayar ka. Normal zakaga yanda yake processing. Bayan ya gama shine zai baka damar saka sunan waka da kuma mawakin da bayanin wakar ko karatun da saurarn su. 


Nasan wasu sun gane dan bayanin da nayi duk da de na dora muku cikakken videon akan youtube da kuma kan facebook page dina. 

Da yawa ma nasan zuwa sukayi domin dakko application din.

To idan link din app din kake nema kaje chan kasa zakaga nace ga links din shine zaka sauke shi a wayar ka.

Amman ga wanda bai ga videon ba gashi nan a kasa kawai ka danna shine videon zai bude ma.

👇👇👇👇👇👇👇

Kamar yanda kuka gani cikin video gaba daya bain babu wani wahala wajen dora dukkanin wakokin ko karatuttukan.


Sannan link din application din gasu nan a kasa zakuga nace Android link idan kana da wayar android to shi zaka taba shine zai baka damar saukewa a wayar ka ta android.

Masu iphone kuma zakuga an rubutu Iphone link shine zai baku damar suakewa akan wayar ku ta iphone.


Android Link


Iphone link


Sannan ga wanda basu da link din asalin audiomack din a kasa zakuga na rubuta Admudiomack for iphone wato na wayar iphone ne.

Sannan masu android zakuga na rubuta Audiomack for android shine na masu android.

Audiomack for android

Audiomack for iphone

Previous Post Next Post