Yanda zaka dauki Sautin sirri kamar a Studio😍 2023

 Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi. Yau darasin mu akan wani application me da zai baka damar daukar murya wadda zakayi amfani da ita batare da angane a waya ka dauka ba.

Da dama akwai mutanen da ke son yin record na muryar su koda ace wasu adduoi ko karatun qur'ani ko waka amman kuma idan sukayi wannan voice din a wayar su gaba daya baya dadi.

Akwai wadanda ma suna da wata basirar da suke so su nuna a social media amman gaba daya basu da wayar da zasu nayin ire-iren wannan abin. Basu da waya mai kyu, Basu da mic nayin record din video ko murya.

 To shi wannan Application din zai taimaka ma matuqa wajen ganin kayi record na kowane kalar sauti sannan ka saita shi da kanka.



Ka cire duk wata hayaniya da take acikin voice din da duk wata isaka kamar a studio ka dauka. Sannan zaka chanja duk kalar muryar da kake so ta cikin wannan application din.


Na kawo wanann Application ne duba da yanda mutane suke kawo gudunmawa na abubuwa a sicial media kamar irin su  nasiha da dai sauran su.

 Shi wannan application din bashi da wahala wajen amfani da shi. Zaka dauki sauti ka gyara shi yanda kake so. Sannan ka dora shi duk inda ka buqata batare da angane a wayar ka kayi ba.

Akwai bangaren video ma shima zaka iya dauka ka cire duk wata iska da haniyar da take a kusa da kai.


Da dai abubuwa masu kyu acikin wannan application.


Ga link dinsa nan a nan kasa zakaga na rubuta Download da koren rubutu sai ka taba shine zaka sauke app din a wayar ka.


👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post