Yanda zaka kalli kowane kalar video ta wannan App din 2023

 


Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a yau a wani sabon darasin.

Yan'uwa yau darasin mu akan wani application daya ne amman tamkar da Dubu domin zai baka damar saukake wahalhalun da muke fama da su bangaren kallon video kowane kala ne. Da dama muna son kallon video ko films haka to amman wani videon baya budewa a wata player din. Player shine irin su VLC,MXPlayer da sauran su. Sai de mutum yai ta rabe-rabe wajen neman wadda zai yi kallon da ita. Hakan yake sakawa mutum zakaga ya tara player da yawa domin kowace tana bude masa kalolin videon da yake buqata.

To wannan application da na kawo mana zai baka damar bude kowane kalar video batare da ka tara player da yawa a wayar ka ba. Sannan kowane kalar Extension  na video. Extension shine kamar 3gp,MOV,MP3 da sauran su.



Bayan nan tazo da nau'oin abubuwa da yawa wanda zai qawata ma kallon naka.

Suna kamar haka.

Na farko zaka kalli kowane video ta cikin wannan player batare da ka chanja kowace kalar player ba sannan duk nauyin video ka kankantar sa.



Na biyu zaka iya casting din video daga wayar ka zuwa Tv din ka. Ko da kana da films ko movie ko wani kalar video zaka iya hada shi da Tv din gidan ka ko office to wannan application zai taimaka ma.



Na uku Zaka iya sakawa videos din naka password wanda babu mai iya budewa. Sai kai kadai saboda sirrikan ka.


Da dai abubuwa da yawa sai ma ka malle ta sannan zaga abin burgewa.

 Zaka iya bude video kana kallo koda ka fita daga app din. 

Sannan ko wayar taka ta shiga security zaka iya kallon videon ta wannan app.

Ga link din Application din nan a kasa zakaga an rubuta Download da zarar ka taba shine zai baka damar saukewa a wayar ka

👇👇👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post