Yanda zaka gano hanyar da ake sauraron kiran wayar ka ko daukar sirrin ka baka sani ba😭. 2023

 Yanda zaka gano hanyar da ake sauraron kiran wayar ka ko daukar sirrin ka baka sani ba😭. 2023



Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a wani sabon darasin wanda zai baka damar kariya daga masu bibiyar ka a wayar hannun ka.

Wato yanzu hacking ya zama ruwan dare wanda za'a iya saka ma wani app domin daukar bayanan ka ko a turama da wani link wanda zai na daukar bayanan ka abinda ya danganchi hoton ka ko kiran ka ko location din ka ko text message din ka.

 Wani lokachin kuma zaka iya ziyartar wani website wanda zai sakama wani abu daban a wayar ka domin daukara bayanan ka baka sani ba.

 To koma dai menene wannan application zai taimaka ma ya baka damar gano duk wani application ko duk wata matsala da take faruwa a wayar ka domin magance ma ita.

 Akan iya saka ma wani application sannan a boye ma shi acikin wayar ka ko kuma ita kanta wayar tazo da application din a wayar amman baza ka ga wannan application din ba saboda akwai hanyoyin da ake bi ake boye app saboda daukar wani sirri acikin waya.



 Da zarar ka mallaki wannan application din zai baka damar ganin wannan application din sannan ka cire shi a wayar ka.

 Kuma idan zaka ga application din akwai inda zaka shiga shi wannan application wanda na kawo muku zaiyi search din dukkanin abinda yake a wayar ka sannan zai ware ma komai daban-daban domin gane matsalar wayar taka.

 Bugu da qari ba iya nan wannan application ya tsaya ba akwai abubuwan lura da yawan gaske acikin sa.

 Saboda amfanin sa ne masa akwai mutane sama da million biyar ne suka dakko application din a playstore 5m+.


Ga link din application din a kasa zakaga an rubuta download d akoren rubutu sai ka taba ka sauke app din a wayar ka domin amfani da shi.

👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post