Yanda zakayi chat da kowane kalar yare ta amfani da AI😍😍TypeAi keybord



 Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi da fatan kowa yana nan lafiya.

 Yau darasin mu akan maganar AI ne wanda zai baka damar chat da kowane kalar yare sannan koda baka iya rubutu ba shi da kansa zai rubuta ma duk abinda kake so koda kuwa baka iya yaren ba.

  Wannan application da zarar ka saka shi a wayar ka zai maqale a keybord din wayar ka inda kake rubutu idan kana chat kenan.

To ta amfani da wannan keybord na AI zaka iya dukkanin yaren da kake so. 

 Bugu da qari koda AI din ne kake so ya rubuta abin batare da kasha wahala ba zaka saita keybord din a matsayin AI da zarar wanda kuke chat dashi ya turo ma sako shi keybord din zayyi masa reply.




 AI dai yanzu ita ake ta yayi zakaga abubuwa da yawan gaske da zasu baka damar amfani da wannan manhaja ta AI website da App da kuma software ta computer. Kai hatta acikin application da software yanzu ana saka AI wanda zaka fada masa abinda kake so yayi ma a wannan software din to da kansa zai saita ma.

Kamar Software ta editing din hoto akwai bangaren AI wanda zaka fada masa abinda kake so yayi wa wannan hoton naka to ita software da kanta zata saita tayi editing din kuma abin burgewa.

 To shine shina aka zo da wannan apolication a matsayin keybord na waya dukkanin inda kake so kayi rubutu inde keybord din ka zai fito to zakayi amfani da wannan manhaja ta TypeAI.



Zan ajje muku links din application din duka na wayoyin guda biyu android da iphone sai ku taba ku sauke shi a wayoyin ku.

 Idan kana da iphone zakaga na saka iphone app sannan idan Android ce ma zakaga na saka Android App.

Sai ka sauke shi a wayar ka kayi amfani da shi.

Download

Iphone App

Android App

Previous Post Next Post