ALL IN ONE OFFICE APP 2023😍😍

 Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a sabon darasin namu.



Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne wanda zai baka damar karanta komai ta cikin sa batare da ka tara Apps da yawa a wayar ka ba.

 Wannan application din ya hada dukkanin Format na decument wanda idan kana so ka bude shi a wayar ka. Zaka iya amfani da application guda daya.

     KARIN BAYANI. : Dukkanin wasu rubutu da muke gani akwai extention ko format da suke zuwa dasu. Duk da nasan Dalibai sai sunfi ganewa akan format din. Amman zan danyi muku bayani kadan domin kowa ya fahimta.

 ire-iren rubututtukan da muke dasu to suna zuwa da format kamar haka. ( PDF. DOCS, Excell,Word, Powerpoint ) Da sauran su.

  PDF: Mutane da yawa sunsan PDF domin saboda yawan amfani da waya ko chat akan turo mana abu a matsayin PDF. Sai de sauran ne inde ba masu hulda da computer ba basu gane format din su ba.

 Duk da zan danyi mana takaitaccen bayani.

 Excell akwai format excell wadda idan aka yi rubutu a software excell sannan ana so koda an turo ma zaka iya edit kachi gaba da rubutawa za'a iya save din sa a matsayin excell din. kodan duk sauran format din ma haka suke.

 Shi de excell ana yin sane wajen tara lissafi. Misali na kasuwa ko na makin jarabawa ko wani lissafi. Akan iya tsarashi ma a matsayin Database a wani app ko website.


Kamar yanda kuka ganin misalin sa a hoton sama.

 Word: kuma anayin sa ne wajen rubuta wani bayani kamar littafi ko project ko tsara jarabawa ( Exam ) ko wani rubutu na daban. Kamar de yanda muke ganin takardu farare manya to anayin su ne  a word: MS word wato ( Microsoft Word ).


kamar yanda kuke ganin misalan word a hoton sama.

Powerpoint: Powerpoint kuma ana yin sane wajen gabatar da wani abu wato Presentation. Gabatarwa kamar a makaranta zaka gabatar da project ko a kasuwa zaka gabatar da wani abu ko kamfani. Shine zaka shiga cikin software ta powerpoint ka tsara ire-iren abubuwan. Sannan wajen gabatarwar ana takaita rubuta. 


kamar yanda kuke ganin misalan Powerpoint a hoton sama.


To dukkanin ire-iren wannan format din na rubutu idan aka turoma batare da ka tura a computer sannan ka nemo software irin format din ba. Ko a wayar ka ka nemo dukkanin applocation na bude kowane format ba.

Wannan Application din zai hade ma dukkanin kowane format wajen karantawa. Ko ka gyara rubutun.


Ga link din sa a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu da zarar ka taba shine zaka sauke shi a wayar ka.


Download

Previous Post Next Post