Yanda zaka bude website a kasa da minti biyar (5) Ta wayar ka

 


Assalamu alaikum warahmatullahi wabarakatuhu. Yan'uwana a addinin muslunchi.

Yau darasin mu ya kamata yan'uwa mu mai da hankali akan sa saboda hanya ce da zata baka damar ka bude ko kirkirar website ta amfani da wayar hannun ka sannan batare da ka iya wani hanyar programming ko wani yare na computer ba.

 Hanya ce kawai da zarar ka mallaki application din ta ciki zai baka damar kirkirar website ka bashi suna sannan ka zabi template din da kake so.






 Bayan ka zabi template din da kake so shine zaka zabi sunan da kake buqata ka yi amfani dashi wajen bude website din. Bayan nan zai baka damar duk chanja wata kafa da kake buqata wadda zaka chire wani suna ko ka dora hoto ko dukkanin abinda kake buqata batare da ka qare wajen amfani da wani yare na computer ta (programming). 

 Sannan idan kana buqatar amfani da domain shi wannan website din zai baka damar maqatala domain kowane kala a price mai sauki.

 Ga link din application din a chan kasa zakaga na rubuta dowload da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.

 Amman kafin nan zan danyi bayani akan ( DOMAIN da kuma HOSTING ). Domin ga wanda basu sani ba.

 Abin ma da yasa na kawo bayanin domain din saboda a kasa nace zaka sayi domain a price mai sauki.

             DOMAIN : 

Domain shine zaka siya kamar abinda ya danganchi ( .com .ng .org .edu ). Da sauran su wanda zakaga yana zuwa a karshen kowane website wanda dole sai dashi za'a iya search din website din naka.

 Amman akwai hanyar da ake amfani da domain a kyuta amman zaka ga da sunan wannan website din da suka baka kyutar misali. ( .xtgem.com ko .wix.com ). To zakaga xtgem da Wix din duk sunan site ne guda. To amman idan kana so ka cire sunan site din sai iya naka shine zaka siya sannan koda ka buqachi wani domain din idan wani yayi amfani dashi to za'a ce ma not available. Kamar de yanda kuke ganin wannan site din nawa kktechtube.com.

       HOSTING

Hosting shine inda zaka ajje website din naka da dukkanin kayayyakin da wannan website din ya kunsa. Hotuna ne ko wakoki ne ko shi asalin site din koda programming kayi ta wajen hosting zaka zuba dukkanin abin da kake so ya kasance a gani acikin website din naka.

Idan zakayi gyara Hosting zaka shiga ka cire hoto ko ka chanja wani abu acikin website din naka.

 Sai de shi Hosting siyan sa sannan ana samun kyuta ( free ). kamar shi wannan Application din da na kawo muku to hosting din kyuta ne. Shi yasa kana bude application din to zakaga an baka template wanda zakayi amfani ka saita website din naka.

 Sannan zaka iya siyan domain a wani website din sannan hosting ma a wani website din ta amfani da sharing din sa.

 Bugu da qari idan kana da hosting a website ko domain to zaka iya chanja shi zuwa wani website din.

 Wannan shine takaitaccen bayanin Domain da kuma hosting.


Ga link din Application din a kasa sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇


Download 

Previous Post Next Post