Yanda zaka cire Apps da yawa a lokachi daya a wayar Android 2023

 

Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi. Yan'uwa da abokan arziki ya hakuri damu. Allah ya shiga lamarin mu ameen.

 Yau darasin mu akan wani application ne wanda na tabbata zakuyi mamakin yanda yake saboda zakaga babu ire-iren wadannan application din. Har sai anyi muku darasi sannan.

Application ne da zai baka damar cire duk adadin da kake so na Application a wayar ka kuma a lokachi daya.

 Mun sani idan zaka cire application (unistall) a wayar ka sai de ka cire daya bayan daya babu damar kayi mark ko ka hada application da yawa a lokachi daya sannan ka cire shi.

 To shi wannan application din da na kawo muku yau zai baka damar hade adadin application da yawa a lokachi daya sannan ka cire shi.




Bugu da qari wannan application din zai rarrabe maka duk application din wayar ka.

 Misali system application sannan kuma da user application.

 Zan danyi muku karin bayani akan user da kuma syetem din.


1) system application : Application ne da yake zuwa tare da waya wanda waya bata iya yin wani abu sai da taimakon wannan application din. To wani lokachin ma gaba daya ba'a ganin su sai de idan ka shiga cikin setting. To kuma akan samu wani ya goge daya daga cikin system app hakan yake sawa wayar shi. Ta samu matsala ta wani fanni.


2) User applocation: Application ne da gama garin mutane suka hada shi sannan aka dora akan wayar. Misali whatsapp, facebook,xender ko games ko wata launcher haka. To su wadannan koda ka cire su basu da wani illa ga waya.

 To shi wannan application din idan ka bude shi zai baka damar gane system app da kuma user app wanda babu yanda zakayi kayi mistake wajen cire shi a wayar ka.



Ga link din application din nan a kasa zakaga an rubuta download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇


Download

Previous Post Next Post