Yanda zaka koyi kowane kalar yare A wayar ka Ta cikin sauki

 Yanda zaka koyi kowane kalar yare A wayar ka Ta cikin sauki



Assalamu alaikum barkanmu da wannan lokachi. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne mai matuqar amfani wanda zai baka damar koyon yare kowane kala a wayar ka ta cikin sauki. Sannan zai fassara duk wani rubutu zuwa yaren da kake buqata.



Application ne da ya kunshi abubuwa kala daban-daban wanda da dama mutane suna buqatar ire-iren sa.

Na farko zaka iya koyon yare da dukkanin wasu hikimomi ko karin magana wanda wannan yare ya kunsa.

Na biyu zai fassara ma duk wani rubutu zuwa yaren da kake so.

Na uku zai baka dama kayi chat ko magana da duk wanda kake so ta cikin wannan applcation koda kuwa baka iya yaren sa ba.



Na hudu zai kowama yanda ake furka kalma idan baka san yanda zaka fada ba. Da zarar ka rubuta shi application din zai furta ma kaji yanda furuchin ta yake.

 Da sauran abubuwa muhimmai. Da dama mukanyi tafiya zuwa wata kasar ko wani garin amman zamuga mun hadu da wani mutumi ko wasu mutane wanda kwata-kwata bama iya jin yaren su. To da taimakon wannan application din zamu iya fira hatta karin magana na wannan yaren zamu iya koya. Bugu da qari harda abinda ya danganchi waka domin zakaga a yare abu biyu yakewa mutane wahala. Karin magana da kuma waka.



 Badai zan cika ku da surutu ba ga link din application din nan a kasa zakaga an rubutu download sai ka taba shine zai baka damar sauke application din acikin wayar ka.


👇👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post