Yanda zaka mayar da WEBSITE Application an wayar Android ka sami kudi dashi

 Yanda zaka mayar da WEBSITE Application an wayar Android ka sami kudi dashi



Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a yau a sabon darasin namu. Yau darasin mu akan wani application da zai baka damar mayar da website zuwa Application na wayar Android sannan ka dorashi a playstore.

 Wannan darasi yana da tsada sosai domin zaka iya kasuwanchi da shi. Wajen saitawa dukkanin masu amfani da website zuwa app na wayar android sannan ka dorashi a playstore.

  Da yawa mutane suna da website ko blogger to amman suna buqatar suga sun mayar da wannan website din zuwa application na wayar android domin amfani ga dukkanin masu amfani da wayar android din.

 To amman zakaga wannan hanyoyin suna da wuya koda ma ace ka sami wanda zai iya mayar ma da website din zuwa App an wayar android zakaga zayyi ma tsada sannan yaqi gama ma da wuri.

 Musamman wannan lokachi da muke da website na siyar da DATA to amman zakaga da yawa bamu da app wanda duk masu amfani da wayar android zasu iya amfani dashi domin sana'ar tamu ta ci gaba. Ballantana ma a dakko a playstore kamar yanda sauran Application suke.

 To shi wannan application zai baka damar mayar da website din ka zuwa application sannan zaka iya dora shi a playstore bugu da wari zakaniya saka Admob acikin application din naka domin google su dora ma talla suna biyan ka kudi.


 Sannan shi wannan Application babu wahala wajen amfani dashi. Da zarar ka bude shi zai baka damar saka link na website din naka sannan ka mayar da shi apps na wayar android.

 Sannan koda baka da website zaka iya sannan ka dinga samun kudi domin zaka dinga hadawa mutane suna biyan ka.



Zaka qawata application din naka domin ga wanda suke amfani dashi baza su taba tunanin ta wannan hanyar kayi amfani da shi ba.

 Ga link din Application din nan a kasa zakaga an rubutu download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka domin amfani da shi.

👇👇👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post