Yanda zaka qawata wayar ka ta koma launi mai kyu abin sha'awa🥰

 

Yanda zaka qawata wayar ka kowace kala ce qara ko babba.

Assalamu alaikum barkan mu da sake kasancewa a yau a wani sabon darasin na mu.

 Yau darasin mu akan wasu launcher ne guda biyu wanda zasu baku damar gyara launin kalar wayar ku. Wadannan Application manyan App ne bayan nan inde ka saka su acikin wayar ka bazasu cike ma space din wayar ka ba.


Da yawa akwai masu buqatar ganin sunyi amfani da wata launcher wadda zata dan gyara musu wayar su domin jindadin amfani da ita. Amman koda sunyi kokarin saka wata launcher din zakaga wannan launcher bayan nauyin da gake da ita zakaga tana nuna talla akan fuskar waya.

Har mutum ya dinga zargin menene yake nuna masa talla acikin wayar sa koda bai shiga ko ina ba.

 Hakan yasa na kawo mana launcher mai inganchi wadda zata baka damar qawata wayar ka sannan babu wata talla ko wani abinda bai dace aciki ba.

         Launcher ko Applocation ?

Nasan wasu zasu ce me yasa nake rubuta launcher bayan application ne na waya android sannan dukkanin wani abu da aka saka shi a wayar android ko iphone ko wata Tablet to ana kiranshi da Application amman ni ina rubuta launcher.

To shi applocation da ake sakawa yake chanja launin waya ana kiranshi da launcher ne koma bayan sauran application da muke sakawa.

 Shi yasa nake tayi muku bayani akan launcher saboda wannan darasi ya kunchi abinda idan ka saka shi zai chanja ma launin wayar taka gaba daya.

Wadannan Application guda biyu duka wanda kayi amfani dashi suna d akyu sosai.
 Sannan idan ka dauki guda daya shina kayi amfani da shi yayi.
Ba sai ka hada duka guda biyun ba.
 Sannan launcher bayan qara kyn waya da take yi kowace akwai abu na daban da take zuwa dashi. acikin ta.
Amman dukkanin hotunan da na dora a sama da kuma zan dora wasu a kasa samfure ne na launcher wadda na fara ajje muku link din ta a kasa ta farko kenan.
 Amman ta biyun itama idan kuka je chan kasa zaku ga yanayin launin da take dashi.



Sannan hoton kasa da zaku gani samfuri ne na launcher ta biyu wadda ita ma zata baka launi mai kyu da kuma abubuwan ban qawa domin amfani da wayar taka cikin sauki.


Dukkanin wadannan launcher din wadanda suke amfani da su a wayoyin su sun wuce miliyoyin mutane duba da yanda suke da abubuwan banqawa acikin su.

 Ga link din su nan  a kasa zakaga Download 1 to shine na ajje muku kalar hoton sa a farko kenan sannan Download 2 shine na ajje muku kalar hoton sa a karshe kenan.

Saboda haka duk sai ka dakko su kayi amfani da su.

Download 1


Download 2

Previous Post Next Post