Yanda zaka TSARA jadawalin ( List ) Rayuwar ka ta cikin wannan Application din 2023

 Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi. Yan'uwa yau darasin mu akan application ne wanda zai baka damar tunama dukkanin ayyukan ka na yau da kullum da kuma saukakawa wajen aikata wani aiki saboda kada ka manta. Shide wannan Application zai baka damar tsara dukkanin abubuwan da zakayi da wanda kake tunanin yi ko da kuwa chatting ko sako ( message ) kake buqata kayi. Zaka iya rubutawa a acikin wannan Application message din da kwanan wata da lokachi. Bayan kayi save din wannan rubutu to shi Application din zai tunama da wannan abinda kake so ka tura.


Zaka iya tsara dukkanin ayyukan ka da dukkanin abubuwan da kake buqata batare da kana tunanin wani lokachi zaizo ka manta ba.

 Domin da zarar ka rubuta dukkanin list din abinda kake so kayi a ranar kuma ka saka lokachi da kwanan wata to shi wannan application din zai tunatar da kar akan wannan aikin ko wannan sakon ko wannan abinda kake so ka tura.


 Kuma abin burgewar anan zaka iya saita duk wani mintuna da lokachin abubuwan da zakayi a guri daya bayan nan zaka iya jera dukkanin kayayyakin da kake so ka siya idan kaje kasuwa ko kaje super market batare da ka rubuta wannan abubuwan ba a takar da ( paper ). sannan ta ciki list din da kayi dukkanin wani abu da ka siya ko ka aikaya zaka iya yi masa maki ( mark ).


 Sannan zaka iya rubuta wani sako ( message ) na gmail ko na normal chat  cikakken rubutu wato ina nufin komai da ya kunshi wannan sakon kawai sai ka daita kwanan watan da lokachin da kake so wannan application din ya tura wanna sakon zuwa wanda ka saita da sunan sa. Batare da kana tunanin ka manta wani abu ba.


Dukkan de wasu tsarika na rayuwar mu zaka iya saita shi a cikin Application.

 Ga link din sa nan a kasa zakaga an rubuta Download da koren rubutu sai ka taba ka sauke shi a wayar ka domin amfani da shi.

👇👇👇👇👇



Download

Previous Post Next Post