Inde kai musulmi ne ka Gaggauta mallakar wadannan Application din 2023

 

Inde kai musulmi ne ka Gaggauta mallakar wadannan Application din 2023

Assalamu alaikum barkan mu da wannan lokachi yan'uwa na a musulunchi.



Yau darasin mu abinda ya danganchi addini da rayuwar mu gaba daya ne domin wasu applocation na kawo mana wanda zasu baka damar koyar yanda addinin ka yake.

Kowane application zan ajje muku link din sa kasa da inda nayi bayanin sa. Bayan ka karanta bayanin app din ka lura a karshe na ajje link din sa.

 Sannan ya zamana dole koda ba wannan application din ba ka iya dukkanin su koda wasu daga ciki ne.

Application ne guda uku wanda kowane babu wanda baisan da su ba domin littafi ne a rubuce aka juya shi zuwa application.

 Application na farko zai baka damar koyon dukkanin wasu azkar wanda akeyi safiya da marece ko nace da yamma.

 Da kuma wasu addu'oi masu ma'ana.

 Wanda ya kamata ka iya su sannan kana yin su dukkanin ranakun da kake rayuwa acikin ta.

 Domin sunzo daga hadisan manzon Allah sallallahu alaihi wasallam da kuma muhimmanchin su da garabasar da suke tattare dasu. 

 Gaskiya ya kamata kaniya wadannan addu'oi na safiya da marece.



 Bugu da qari wannan appication din zai iya karanta maka dukkanin wata addua wadda ka gagara iya karantawa har ka kowa sannan akwai su a rubuce a jikin app din.


Shi wannan application ma azkar ga link din sa nan a kasa sai ka taba ka sauke shi a wayar ka.

👇👇👇👇👇👇

AZKAR Download

Wannan Application na Arbauna Hadith: application ne da yake kunshe da hadisai wanda suka danganchi Arbauna hadith wanda dukkanin musulmai nagari su san dashi. Domin hadisai ne guda arbain wanda suka inganta.

 Shi yasa na zabo mana wani application wanda zaka iya koyon Hadisai acikin sa. Tun daga na farko har zuwa guda arbain din da suke a cikin littafin arbauna Hadith.


 Wannan Application ya zama dole sai ka iya abubuwan da yake ciki na hadisin Manzon Allah sallallahu alaihi wasallam.

Saboda haka na ajje muku link din wannan Application gashi nan a kasa zakaga Arbauna Hadith Dowload sai ka taba shine zaka sauke shi acikin wayar ka.

👇👇👇👇👇👇

Arbauna Hadith Download

Application na gaba kuma na karshe sha kundun kenan wanda shine al'qur'ani mai girma. Wanda ya zama dole sai ka iya shi da kuma sannan ma'anar wasu daga cikin ayoyin sa.

 Shi yasa na zabo mana wannan application na Ai tarteel wanda zai baka damar koyon qur'ani tun daga farko har zuwa karshe sannan yayi ma gyara inda baka karanta daidai ba.


Shi wannan Application anyishi ne a matsayin AI wato wanda ake yayi wanda zakayi abu dashi kamar mutum kenan.

 Sannan shi wannan application din zaka iya karanta masa wata sura ko Aya inde ka karanta daidai to normal zai fadama daidai ne inda kuma kayi mistake zai fadama adadin gurin da kayi mistake sanann ya gyarama.


Sannan zaka iya saitawa yanda zaka iya bayar da hadda ko karanta wani adadi na shafi ko Aya duk rana ta cikin wannan Application din.


 Wannan application yana da muhimmanchin da ya kamata ace ka dakko shi sannan kayi amfani dashi.

Ga link dinsa nan a kasa Zakaga an rubuta Qur'ani Dowload da koren rubutu da zarar ka taba shine zaka sauke shi a wayar ka kayi amfani da shi.

👇👇👇👇👇👇👇

Qur'ani Download


Wadannan application ya wajabta ka iya abubuwan dake cikin su domin tsira duniya da lahira sannan kuyi share din videon da kuma darasin zuwa yan'uwa musulmi.

Previous Post Next Post