Tabbas ana bibiyar sirrin wayar ka baka sani ba duk inda kake baka sani ba.

 

Tabbas ana bibiyar sirrin wayar ka baka sani ba duk inda kake baka sani ba.




Assalamu alaikum barkanmu da warhaka yan'uwa barkan mu da sake kasancewa a yau a sabon darasin namu.

 Yan'uwa darasin mu akan wani application ne da zai baka damar gane dukkanin kafar da aka bi ana bibiyar ka ana daukar sirrin videon ka baka sani ba.

  Da yawa akan saka wata device ko camera tayi record din ka misali maganar ka ko motsin ka ko videon ka gaba daya baka sani ba. Kuma akanyi amfani da hanyoyi daban.

 Akan iya amfani da qaramar camera kamar biro ko dan karamin wani abu kamar a ajje ma a dakin ka ko office din ka ko shagon ka ko a hotel idan kaje ko a saka a gaban ajjihu domin daukar sirrin ka.

  Kuma kai bazaka taba ganewa ba. Sai de kaga ana yi maka barazana akan wani videon sirri da aka dauka baka sani ba.

 Domin kayi musu abinda kake so. Ko kuma a yada videon a social media. Domin bata maka suna.


 Zakayi amfani da wannan application wajen gano duk wani camera ko wani abu da ake daukar videon ka baka sani ba. Shi wannan application din zai nuno maka sannan ya sanar da kai wannan abin camera ne. Koda meeting zakayi da wani idan zaka iya kunna application din a wayar ka shi app din zai sanar da kai.

 Sannan koda a dakin da kake ko shagon da kake ko cikin motar da ka shiga duk da taimakon wannan application din zaka iya ganewa.


Application din babu wahalar amfani da shi domin kana budewa zakaga ya nunoma misalin kamar yanda na ajje muku hoton sa a sama.

 Bayan nan koda kana buqatar ka gane ya ake amfani da application din zaka ga tips din yanda zasu nuna ma.

 Bugu da qari zaka iya fadawa application din a ina kake a lokachin kamar yanda kuke gani a hoton kasa.


 Application din yana da amfani sosai musamman manyan mutanen da ake buqatar wani shaida domin a bata musu suna. Zasu iya amfani da wannan application din domin gane duk wani abu da aka saka musu ana daukar videon sirri basu sani ba.

 Link din Application din yana kasa zakaga an rubuta Downlod da koren rubutu da zarar ka taba shine zaka sauke shi akan wayar ka sannan kayi amfani dashi.

👇👇👇👇👇👇👇

Download


Karin hotunan yanda cikin application din yake.




Previous Post Next Post