Yanda zaka hana ayi tracking din ka. A Gano Inda kake

 Yanda zaka hana ayi tracking din ka. A Gano Inda kake

Assalamu alaikum barkan mu da warhaka. Yan'uwa yau darasin mu akan wani application ne da zai baka damar chanja location duk kasar da kake so.

 Ina nufin ka chanja location asalin inda kake ta cikin wayar ka zuwa wani gurin yanda koda kayi amfani da wani website ko social media baza'a gane daga ina kake amfani da wannan manhaja ba.

 Dukkanin wani website da kake shiga ko wani social media akan iya gano daga inda kake amfani da wannan manhaja ko platform ta amfani da location din wayar ka.

 To shi wannan Application din da zarar ka saka shi acikin wayar ka sannan ka zabi kasar da kake so ta cikin wayar ka to zaka iya ziyartar dukkanin inda kake buqata na app ko website ko wata browser wanda babu wanda zai gane daga ina kake ballantana yayi tracking din ka.


Da zarar ka bude applocation din kawai zai nune ma wajen inda zaka zabi address din da kake so kayi amfani da shi. Bayan ka zabai zai muno ma wajen connect.


Da zarar ka danna Connect din kamar yanda kuke gani a hoton da to shikenan ka chanja location din da ka zaba. Sannan zai nuno ma connected.


 Kamar yanda kuke gani a hoton sama to sai ka fita daga app din sannan ka ziyarchi dukkanin wani website ko browser ko wani social media batare da angano duk asalin inda kake ba.

 Illa iyaka za'aga inda ka zaba acikin wannan application din.


 Amman wata kasar zai nuna ma ba free bane dai ka biya sannan zakayi amfani da wannan location din.

 Normal ta wannan application zaka iya chanja location duk inda kake buqata.

 Ga link din application din a kasa zakaga na rubuta Download da koren rubutu sai ka taba shine zaka sauke application din acikin wayar taka sannan kayi amfani dashi.

👇👇👇👇

Download

Previous Post Next Post